Shin Kunsan Dalilin Da Yasa Mata Ke Saka Jigida (Waist Beads)?

Shin Kunsan Dalilin Da Yasa Mata Ke Saka Jigida (Waist Beads)?
 Da Yasa Mata Ke Saka Jigida (Waist Beads)


Dalilin Da Yasa Mata Ke Saka Jigida A Kugunsu wanda bincike A Nigeria ya nuna a kalla kaso 18.7 ke amfani da ita


A baya nasha tambayar kaina ko menene dalilin da yasa mata ke saka Jigida, amma zuwa yanzu na gano wasu dalilan da yasa matan ke saka Jigida bayan gudanar da bincike ta hanyar tambayoyi kai tsaye ga matan. 


Bincike ya gano a kalla kaso 18.7 na matan Nigeria da kaso 47.5 na matan sauran kasashen Afrika ke saka Jigida. A yau zan bayyana muku wasu dalilin da yasa mata ke saka Jigida kamar yadda na samu bayani daga garesu. 


Jigida ana kiranta da suna da yawa a gurare da dama, ana kiranta da belly beads, waistline beads, ko beaded waist chains. Jigida ta zama wani abin yayi da mata da yawa ke amfani da ita suna daurawa a kugun su. Duk da cewa maza da yawa basu san dalilin da yasa mata ke saka jigida ba, amma su matan sun san amfanin da take yi musu sosai. 


 Dalilin Da Yasa Mata Ke Saka Jigida 

Tun a karni na 20 mata suke yin amfani da jigida a kugunsu saboda wadannan dalilan kamar haka 


1. Mata suna saka jigida ne don su san idan girman kugunsu (hip) yana karuwa ne ko kuma raguwa(weight loss or gain in their abdomen) 


2. Ado; A Wannan lokacin ba mutanen Afrika bane kadai Ke saka jigida ba har mutane kasashen turai, Asia, da Amurka na yin amfani da Jigida a Kugunsu saboda suna yin kyau ga duk macen da ta saka. Wato dai mafi akasarin mata suna saka jigida kawai don kwalliya. 


3. Idan kaga mace ta saka jigida alama ne dake nuna ita ba yarinya bace za ta iya haihuwa da zaman aure. Wato yana daga cikin alamar balagar mace idan ta saka jigida a kungunta. 


Wannan sune daga cikin dalilin da yasa mata ke saka jigida (Waist Beads) a kugunsu kamar yadda wasu daga cikin matan suka bayyana min. Idan kuna da wasu dalilan kuna iya bayyana mana su a sashin sharhi.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

2 Comments

Previous Post Next Post