Shin Kunsan Abinda Ke Faruwa Da Maza Idan Suka Dauki Lokaci Ba Su Yi Jima'i Ba?

Shin Kunsan Abinda Ke Faruwa Da Maza Idan Suka Dauki Lokaci Ba Su Yi Jima'i Ba?
Abinda Ke Faruwa Da Namiji Idan Ya Dade Bai Jima'i Ba 


Shin Kunsan Me Ke Faruwa Da Maza A Lokacin Da Suka Dauki Lokaci Ba Su Yi Jima'i Ba? 


Jima'i yana yi ne na halitta kuma al'amari ne da ya shafi lafiyar mutum, amma shin mai zai faru idan maza suka dauki lokaci ba tare da sun yi Jima'i ba? Sakamakon yana iya kasance na fili da badini, kuma suna shafar walwalar namiji. A Wannan rubutun za mu kawo muku abubuwan dake faruwa da namijin da ya dade bai yi jimai ba. Za mu bayyana muku irin canjin da mutum zai ji a Jikinsa da kuma rashin samun kwanciyar hankali. 


Abinda Ke Faruwa Da Namiji Idan Ya Dade Bai Jima'i Ba 

Rashin yin jima’i musamman ga namijin mai aure yana haifar da wasu matsaloli na lafiya da masu bincike suka bayyana, ga su kamar haka. 

 

A cewar binciken lafiya, idan maza suka dauki lokaci ba tare da sun yi Jima'i ba jikinsu yana samun canji, misali 'ya'yan maraina suna kankancewa, wanda hakan ke saka damuwa, karfin jiki na raguwa. Mazan da suke daukar lokaci ba su yi jimai ba na fuskantar raguwar gudanar jini a al'aurar su wanda ke haddasa raguwar girman al'aura. 


Bugu da kari, rashin gudanar da jimai ga maza na iya haddasa musu damuwa da yawan tunani wanda kan iya jawo rashin kuzari da gudanar da al'amuran yau da kullum. Sannan kuma namiji na samun kansa cikin tashin hankali da yawan jin haushi. 


Sannan kuma, alamu da ake gani na zahiri ga mazan da suke daukar lokaci ba su yi Jima'i ba shine, wasu mazan suna yin dabi'u kamar na marasa hankali. Wasu kuma suna jin rashin yadda akan kansu. Wani kuwa yana jin yin nesa da mutane ya kasance shi kadai. 


Sai dai an bayyana cewa halin da mazan da basa yin Jima'i ke shiga ya danganta da kowane mutum, kuma ba duka maza ne ke samun kansu a irin wannan halin da muka bayyana ba. Sannan idan kana daga cikin masu samun kansu cikin wannan yanayin da muka bayyana ku yi kokarin tuntubar likita don baku shawarwari kan abubuwan da ya dace. 


Daga karshe sakamakon rashin yin Jima'i na tsawon lokaci na iya shafar lafiyar maza ta bangarori da dama, wasu kuwa damuwar ta dan lokaci ne. Fahimtar irin halin da namji ke shiga a dalilin rashin yin Jima'i zai taimaka muku wajen daukar matakin da ya dace. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post