Shawara Ga 'Yan Mata Da Zawarawa Masu Shirin Yin Aure

Shawara Ga 'Yan Mata Da Zawarawa Masu Shirin Yin Aure
Shawara Ga 'Yan Mata Da Zawarawa Masu Shirin Yin Aure 


Ba laifi bane in kinyi bincike akan sana'arsa dan ki tsaftace abinda zai kawo miki dake da 'ya'yanku ku ci. Anaso kuma kema ki kasance da wadannan abubuwan uku 3


Kowace mace bataso ace a yau tayi aure, a samu gobe ta fito daga gidan mijinta. Sannan ko wace mace takanso tayi alfahari da uban 'ya'yanta, a sameshi mutumin da ya hada abubuwa uku 3, haka shima yanaso ace matarsa ta hada abubuwa uku 3, sannan tafishi da abubuwa uku 3, shima ya fita da uku 3. Wadannan abubuwa (12) in har akayi sa'a ma'aurata suka hadasu, toh aure yakan dade bai samu tangarda ba. Yake 'yar uwa, ki fara duba wadannan abubuwa uku 3 a halayyarsa wanda kikeso ya zama mijinki. Wadannan abubuwa uku sune:


1. Amanarsa

2. Addininsa

3. Gaskiyarsa


Ba laifi bane in kinyi bincike akan sana'arsa dan ki tsaftace abinda zai kawo miki dake da 'ya'yanku ku ci. Anaso kuma kema ki kasance da wadannan abubuwan uku 3. dan dasu ne mutum yakan zama mutum, amma idan mutum yarasa su to ya zama mutum mutumi. Basai kinsa a binciko miki wadannan abubuwan ba, ke da kanki zaki gansu a gurin saurayinki. A lokutan da yake zuwa tadi, ko kuma kuke magana dashi ta waya. Amma kamar sana'a zaki iya sawa a bincika miki.


Yadda Zanyi In Samu Miji Mai Addini, Da Gaskiya, Da Amana 

Ki lura daga lokacin da yake zuwa gurinki kuke hira, yadda zaki gane amanarsa? wane irin zama kuke yi? a mota ko a parlor ko a zaure ko a daki? Akwai tadin da ake kira 'No Gap' ko kuma 'Bamba to Bamba' ko kuma 'shan ice-cream'. In har kunayin daya daga ciki yakamata ki tambayi kanki shin zai zama mai amana kuwa? Ya kamata kiyi koyi da matar Annabi Musa AS, matakan da tabi ta zabeshi a matsayin mijin aure. Sun sameshi a matsayin bako sannan ya nuna masu jarumtaka a lokacin da suka zo zasu shayar da dabbobinsu, suka sami rijiyar ta cika da maza majiya karfi suna shayar da dabbobinsu.


Annabi Musa yana waje daya a zaune shima ya lura da kamar 'yan matan ba suje sunyi cudanya da maza ba. Wannan yasa su mazan suka tsanesu suke shayar da dabbobinsu suke hanasu su shayar da nasu. Bayan sun tafi sai, Annabi Musa AS yace da 'yan matan;"mai zai hana kuma ku shayar da naku?" suka ce, "ba muda karfin da zamu iya bude rijiyar dan kuwa maza masu karfi sai sun kai 40 suke iya bude ta". Annabi Musa ya taso shi kadai ya bude musu suka shayar da dabbobinsu. 


Bayan sun koma gida suka ba mahaifinsu labari, yace su kirawo shi. Koda suka zo suka ce masa; 'bawan Allah babanmu yana kira dan ya biyaka abinda kayi mana'. Duk da bako ne shi bai san ko ina a garin ba, bai yadda yasa su agaba ba yana bayansu, sai ya wuce gaba suna binsa a baya har suka isa gidan. Suna zuwa suka cewa babansu ka dauke sa aiki sannan ka aura masa daya acikin mu domin mutumin na da karfi da amana. Sai ya tambayesu ya akai kukasan haka? suka bashi labarin karfinsa wajen bude rijiya, amana kuma ta wajen tafiyarsu zuwa gida. Shima kuma annabi Musa AS nan take ya yarda saboda ya lura da tarbiyar 'yan matan da ya gani. Nan take har yabiya sadakin da yafi komai tsada a lokacin; shine kiwon dabbobi na shekara goma (10) a matsayin sadaki.


Don haka ina mai baki shawara daki so mijin da yake kaunar ki ba sha'awar ki. Sai na biyu;


Gaskiyarsa 

Ki lura cikin maganganunsa ko yanayin karya dan ya burgeki. Misali ya aro mota ko kuma kayan sawa ko kuma kudi ko kuma makamantansu. Sannan ki lura cikin maganganunsa da kukeyi a waya ko a fili, karyace tafi yawa ko kuwa gaskiya? sai kuma ki lura abubuwa nawa yayi miki alkawari ya cika miki? in yanada mata kar ki yarda ya rinka zaginta a gabanki kina mara masa baya, ko kuma ki rinka jin dadin yana zagin matarsa. To kemafa wata rana ke zai zaga awajen wata dan haka sai ki kiyaye.


Addininsa 

Zaki fi kowa saurin fahimtar mijinki ko saurayinki mai addini ne ta wajen hira. Yakan amfanar dake ta wajen yadda zaki gyara tsakaninki da mahaliccinki? ko kuwa holewa kawai yake karantarwa in ana waya ko kuma yazo hira? sannan ki lura sau nawa kuna hira lokacin sallah yayi ya umarceki da ki tashi kije kiyi sallah shi kuma ya tafi masallaci? Duk irin wadannan yakamata ki lura dasu awajen mijin da zaki aura, duk da ba rubutasu akeyi a goshi ba.


Akwai abubuwa uku da yakamata mata tafi mijinta dasu

1. Tafishi yarinta

2. Tafishi karamar murya

3. Tafishi kyau.


Duk da cewa wadannan ba aya bane ko hadisi suka kawo hakan ba, kawai magana ce ta malamai masana ilimin rayuwar 'dan Adam suka fada. Zaka ga akwai hikima a maganarsu.


Sai kuma inda yakamata kuyi tarayya da matarka. Zataso ace tayi tarayya da mijinta ta wajen wadannan abubuwa guda uku (3);


1. Addininku ya zama daya

2. Akidarku ta zama daya

3. Tsaftar ku itama ayi sa'a tazama daya.


Idan akai sa'a wadannan abubuwan sun hadu wajen ma'aurata, to su yi shimfida a rinka zuwa ana yi musu murna. Domin zai yi wuya kaga aurensu ya samu tangarda. Muna rokon Allah SWT ya taimake mu da iyalenmu baki daya ameen.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post