Sanin Kalmomin Soyayya Da Kauna Da Mace Za Ta Yiwa Namiji

Sanin Kalmomin Soyayya Da Kauna Da Mace Za Ta Yiwa Namiji
Sanin Kalmomin Soyayya Da Kauna Da Mace Za Ta Yiwa Namiji 


A sami wani lokaci idan zakiyi masa magana ki kirashi da wani suna na soyayya. Zaki iya kiranshi da sweetheart, honey ko baby, masoyina ko sahibina, nawan, kodai wata kalmar da zata faranta masa rai


Idan kina so mijinki ya kaunace ki, sai kin iya kalmomin kauna da soyayya. Anaso ya zamana kinsan kalmar da zaki fadi ma maigida, kalmar da zata kara jefa kaunarki da soyayyarki a zuciyarsa. Ki rinka nuna masa irin soyayya da kaunar da kike masa, ita zata zamo sinadarin kauna da soyayyarki a zuciyarsa, wannan a dole sai kin koya. 


A sami wani lokaci idan zakiyi masa magana ki kirashi da wani suna na soyayya. Zaki iya kiranshi da sweetheart, honey ko baby, masoyina ko sahibina, nawan, kodai wata kalmar da zata faranta masa rai, wata kalmar idan kin fada masa in yana jin nishadi to zai yi maki abinda zaki dade kina alfahari dashi.


Yanada kyau mata suyi koyi da Aisha RA. Lokacin da Manzon Allah SAW ya bata labarin Ummu Zarrin, yadda mijinta yake sonta yake kaunarta, yake kyautata mata, da ya gaya mata sai yace: 'ai a gurinki kamar Ummu Zarrin ne da Abu Zarri. Aisha tana daga kai ta kalle shi tace; ya Manzon Allah wanene Abu Zarrim? kafi alkairi fiye da Abu Zarrin ga Ummu Zarrin aguri na ya Rasulullah', wannan kalma ce ta kauna da nuna soyayya.


Anaso dole kisan yadda zaki nuna ma mijinki kauna da soyayya. Wannan yana daga cikin abinda yake kara dankon kauna da soyayya a cikin zaman aure. Yana sanya miji yaji da zarar yabar inda kike yaji babu abinda yake tunani sai ke.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post