Rabe-Raben Jinin Dake Fita Daga Al'aurar Mata |
Jinin dake fita daga al'auar mace ya rabu zuwa 3 ko 4, kuma ba duka mata ne ke iya bambance zuwan jini ba musamman ga matasan mata sabuwar balaga. Hakan yasa na tattaro muku yadda za ku gane rabe-raben fitar jini daga al’aurar mata.
Jinin Budurci
Shine jinin da yake zuwa a sakamakon Fashewar tantanin budurcin mace. To, idan jinin ya zo wa mace sai ta kasa gane cewa, shin jinin da ta gani na Bukhara ne, ko kuwa jinin Haila ne? Yaya za ta iya Bambancewa?
Gwaji
Idan mace ta rikice, ta kasa gane matsayin Wannan jini, sai ta sanya audugarta, ta bar ta a jikinta zuwa wani lokaci. Daga nan, sai fito da ita ta yi nazarin ta idan audugar ta kasance, mudawwi'atun da jini, watau jinin a kewaye yake a jikin audugar bai ratsa tsakiyar audugar ba, to Wannan jini, jinin Bukhara ne.
Amma idan ta fito da audugar, ta gan ta 'mungamisatun, da jini, watau jinin ya mamaye audugar gaba daya, to Wannan jinin Haila ne.
Jinin Ciwo
Idan mace tana dauke da wani ciwo a cikin cikinta, wanda yake fıtar da jini ko kuma ciwon ya kasance a cikin al'aurarta kuma yana fitar da jini. To, a Wannan yanayi, sai Mace ta rikice, ta kasa gane cewa, jinin da ya zubo a yanzu, jinin Haila ne, ko kuwa jinin ciwon ne da Ke jikin ta ne? Yaya za ta yi?
Gwaji
A nan ita ma za ta yi gwaji, watau, sai ta sanya audugarta, ta bar ta zuwa wani dan lokaci, sannan ta fito da ita. Idan ta fito da ita, sai ta lura da kyau ta ga jinin yana fita bangaren dama ne, ko ta bangaren hagu? Idan ta bangaren dama ne, ko ta bangaren hagu? Idan ta bangaren dama yake fita, to jinin na Wannan ciwon nata ne. Amma idan ta bangaren hagu yake fita, to jinin Haila ne.