Nau'in Yadda Tantanin Budurci Yake

Nau'in Yadda Tantanin Budurci Yake
tantanin budurci


Nau'in Yadda Tantanin Budurci Yake Da Kuma Yadda Ya Bambanta A Jikin Mata 

Tantanin budurci, wata 'yar fata ce ko kuma raga da take toshe da kofar farji ta kasa daga waje, kuma dunbarun farji suna kange da ita. tantanin, kamaninsa (siffofinsa) sun bambanta daga wasu matan zuwa wasu.


Amma wanda ya fi yawa a tsakanin 'yan mata, shine wanda yake da wata huda-huda kewayayya a tsakiyarsa, wadda girman wannan huji ya sha bamban a tsakanin mata, sai kuma mai kamar wata-wata, a farkon kamawarsa har zuwa ya yi kwana 5, wannan kuma kofar da take tsakiyarsa kamar wata take.


 Sannan kuma mai raga-raga, wannan shi kuma kananan kofofi da dama ke kareshi, kamar dai yadda raga take. tankan yiwu a haifı yarinya ba tare da kofa ko huji ba, a tsakiyar tantaninta. wato kenan kofar farjinta ta zama a toshe dundum. yarinya mai irin wannan dundadden tantani, idan ta balaga ta fara yin jini, jinin zai rika taruwa a cikin farjinta, wanda daga karshe dole sai likita ya yi mata aiki, ya bude kofar ya fitar da jinin da ya taru. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post