Nau'in Nama Da Ake Bukatar Mutanen Dake Dauke Da Ciwon Sugar Da Hawan Jini Su Ci

Nau'in Nama Da Ake Bukatar Mutanen Dake Dauke Da Ciwon Sugar Da Hawan Jini Su Ci


Nau'in Nama Da Ake Bukatar Mutanen Dake Dauke Da Ciwon Sugar Da Hawan Jini Su Ci 


Idan kana da ciwon siga ko hawan jini, dole ne ku kula da irin abincin da kuke ci. Wasu abincin suna haifar da rashin lafiya, musamman nama da yawan Kitse da gishiri. Amma akwai wasu nau'in nama cin su baida illa. 


- Naman Kaji, wadannan nau'in nama ba su da yawan kitse da kan iya haifar da matsala ga zuciya. Sannan suna dauke da sinadarin protein wanda kan taimaka wajen rage siga. Kuna iya sarrafa naman kaji ba tare da amfani mai da yawa ba kamar yin gashi da sauransu. 


- Kifi mai dauke da omega 3, cin irin wannan kifin yana taimakawa wajen rage kumburin jiki, rage hawan jini, kifi irin sardines, mackerel suna da tasiri ga jiki. Ana son a ci kifi a kalla sau 2 a sati. Kuna iya grika su a haka ba tare da kun yayyanka su ba, kamar gasa su. 


- Naman Sa, cinyar naman sa na daga cikin wajen da babu Kitse, sannan naman kewayen ido na taimakawa sosai domin basa dauke da Kitse. Ana son a dinga ci amma gashi ake da bukata. 


- Naman Tsintsaye, kamar su agwagwa da suke da farin nama da protein. Kuna iya cin su a wasu lokutan amma ba da yawa ba 


Idan kukai Zabi irin naman da za ku dinga ci, yana da kyau ku yi tunanin yadda za ku dinga sarrafa su. Kada ku soya su da mai masu illatarwa, saboda suna iya haifar da yawan mai wanda ke iya haifar da illa ga jiki. Sannan kuna iya yin amfani da abincin gargajiya wanda kan iya taimakawa jiki.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post