Nau'in Maza 5 Da Mata Ke Tsoron Rabuwa Dasu |
Mata suna shiga damuwa idan sun rasa namijin da ya zama abokin shawara ko mai taimaka musu a zamantakewar rayuwa
Mata kamar yadda maza suke suna da fargarbar rashin tabbas a soyayya ko a zamantakewa. Sannan yana da muhimmanci ku tuna kowane mutum ya bambanta da wani, ga wasu nau'in maza 5 da mata ke tsoron su rasa su a yayin soyayya ko zaman rayuwa.
Nau'in Maza 5 Da Mata Ke Tsoron Rabuwa Dasu
1. Mai Bayarwa; A koda yaushe mata na fargarbar rasa wanda ke basu musamman abinda ya shafi bukatar kudi ko bukatun yau da gobe. Irin wannan mazan suna samar da kwanciyar hankali da tsaro ga macen da suke tare da ita, shiyasa mace bata son rasa irin wannan namijin koda kuwa ba aurenta zai yi ba.
2. Mai Kulawa; kulawa a soyayya ko zamantakewa babban abu ne, mata na tsoron rasa irin wannan namijin wanda koda yaushe yake tare da ta kodai ta waya ko sakon text ko abinda yai kama da haka. Ita mace tana son kulawa musamman daga wajen masoyinta.
3. Mai Kareta (Protector); Mata da yawa suna jindadin kasancewa da masoyi ko aboki wanda zai kula dasu ya kuma kare su daga dukkan wata barazana da wani zai iya yi mata. Irin wannan mazan ba wai don karfinsu kawai ba amma saboda jajricewar su wajen Kareta daga dukkan wata barazana.
4. Mai Son Cigaba; Mata na son samun namijin dake son tallafa mata wajen cigaban rayuwarta da karfafa mata gwiwa kan abubuwan da take yi wanda zai kawo mata cigaba. Mace na fargabar rasa namiji mai karfafa mata gwiwa don ci gabanta.
5. Abota (Best Friend); abota mai karfi na daga cikin abinda ke tabbatar da kauna tsakani mace da namiji. Namijin da mace bata soyayya dashi amma yakan iya kasancewa babban amini wanda zata iya bayyana masa sirrin ta na dadi ko akasin hakan tare da tattauna muhimman abubuwa. Irin wannan namijin yana shiga ran mace kuma rasa shi babbar barazana ce.
Wannan sune nau'in maza 5 da mata ke shiga fargaba idan suka rasa su, shin kuna da karin bayani ko kuma wasu abubuwan da za ku kara kan wannan da muka bayyana? Ku bayyana ra'ayoyin ku a sashin sharhi.
Kuma haka Domin Nima Naga irin wannan Tafaru Da ni
ReplyDelete