Nau'in Abinci Da Ba'a So A Ci Lokacin Da Za'a Yi Jima'i

Nau'in Abinci Da Ba'a So A Ci Lokacin Da Za'a Yi Jima'i
Abincin dake rage jindadin jimai

Masana sun bayyana Nau'in Kayan abincin dake hana ma'aurata jindadi da samun gamsuwa yayin Jima'i 


Cin wasu nau'in abinci na iya jawo rashin gamsuwa da jindadin jima’i ga ma'aurata. Yayin da kuma cin wasu nau'in abincin ke kara kuzari, nishadi da kuma saka gamsuwar Jima'i. Don samun jindadin jimai da gamsuwa yana da muhimmanci ku kauracewa cin wasu nau'in abinci da abin sha kafin ko lokacin da kuke son yin jimai. 


Yana da muhimmanci ku Kauracewa kayan abinci kamar giya, ko wanda suke kumbura ciki irin abin sha masu gas, sannan cin abinci mai nauyi da shan ruwa da yawa. 


Nau'in Abinci Da Ba'a So A Ci Lokacin Da Za'a Yi Jima'i 

A cewar binciken Healthline, giya na kara gusar da yanayin jindadi sannan yin amfani da ita da yawa yana rage Kuzari. Tana rage karfin jiki da karfin gudanar da jimai. Haka kuma giya tana rage zakuwar mutum yayin jima’i wanda ba lallai a samu gamsuwar da ake bukata ba. 


Cin abinci dake saurin gamsar da ciki kafin Jima'i kamar irin na flour suma suna iya haifar da rashin gamsuwa a yayin jima’i. Sannan cin abinci mai nauyi yana haifar da kasala da cin abinci mai yaji. Suna haifar da rashin kuzari wanda ke haddasa rashin gudanar jini dake rage samun jindadin jima’i. 


Daga karshe yana da muhimmanci ku Kauracewa sha ko cin nau'in abinci dake da tasiri wajen samun gamsuwa kafin yin jima’i. Irin abincin da zaku Kauracewa ci kafin saduwa sune kamar giya, abinci mai nauyi, da abinci mai yaji da kayan sha masu gas. 


Abincin da ya kamata ku ci kafin yin Jima'i sune kayan marmari kamar su kankana, gwanda, ayaba, abarba lemo da sauransu. Sannan cin kayan lambu kamar na ganye suna da tasiri wajen kara karfi da samar da gamsuwa tsakanin ma'aurata.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post