Nau'in Abin Sha Da Maza Za Su Dinga Amfani Dasu Don Magance Rashin Karfin Al'aura |
Kalolin Abin Sha Dake Taimakawa Namiji Samun Kuzari Da Karfin Al'aura
Rashin kuzari ko rashin karfin al'aura ga maza wanda a turance ake kira da "Erectile dysfunction", yanayi ne da namji ke samun kansa na rashin mikewar gabansa. Bincike ya tabbatar da kalla mutane Miliyan 30 ne ke fama da wannan matsalar ta rashin karfin al'aura. Dalilai da yawa na haddasa ko yin tasiri kan matsalar Kuzari. Ga wasu daga cikin abun sha dake magance matsalar karfin al'aura
Akwai wasu dalilai dake sa Kauracewa shan madara, kamar zaki dake iya haifar da rashin sha'awa, amma masana lafiya sun ce baza a iya kin shan madara don rashin karfin al'aura ba. Shan madara na taimakawa da karfin jima’i cewar wani bincike da akai a 2003. Madara nau'i ne na kayan gona(diary) dake taimakawa karfin jiki da gudanar jini, cewar binciken.
Abinda yafi motsa al'aura da kara karfin Kuzari ita ce kankana(watermelon), ana ganin kankana a matsayin abinci amma idan aka yi lemo da ita ta bayar da dandano mai dadi sannan tana taimakawa wajen saurin gudanar jini a jiki sannan tana taimakawa karin samun Kuzari a yayin Jima'i.
Ka yi kokari ka dinga shan lemo irin na kayan gona kamar su abarba, lemon zaki, lemon kankana, da sauran su. Kana Iya hada su gabaki daya a yi maka lemo dasu ka dinga sha akai-akai, suna taimakawa sosai wajen kara lafiya da Kuzarin gaban namji da kuma karfin gudanar da Jima'i.
Allah sa mudace
ReplyDelete