Karin Ni'ima |
Wannan hadin shi ake kira da 'bita zai-zai'. Sirrine wanda yake kawowa mace ni'ima, koda ace irin matan nan ne wadanda basuda ni'ima
Irin wannan hadin shine ake kira da 'Linzamina'. Yana matukar saurin kawowa mace ni'ima, don yin wannan hadin za ku samu wannan abubuwa:
- Zogale
- Zuma
- Nono
Yadda ake hadawa:
ki busar da zogalenki amma ba acikin rana ba, sai ki daka shi yayi laushi sosai. Zaki iya tankadewa. Sai ki rinka dibar cokali daya kina zubawa a nono, ki zuba zuma cokali uku aciki ki rinka sha. Wannan hadin yana matukar karawa mace ni'ima da lafiya sosai.
Hadin Bita Zai-Zai
Wannan hadin shi ake kira da 'bita zai-zai'. Sirrine wanda yake kawowa mace ni'ima, koda ace irin matan nan ne wadanda basuda ni'ima. Yana karawa mace dadi, idan maigida ya sadu da ita ya rude don dadi. Ku samu wadannan abubuwa kamar haka;
- Bawon kankana
- Saiwar zogale
- Kanunfari
- Mazarkwaila
- Zuma
Yadda ake hadawa:
Zaki hadasu guri guda ki tafasa su, in sun dahu sai ki tace ruwan ki mayar da ruwan acikin tukunya, sai ki zuba mazarkwaila da kanunfari. Idan yasamu 'yan mintoci sai ki sauke ki rinka sha. Zakiji ki kinyi fanjam da ruwa da yardar Allah.
Kafata Kafar Ki Uwargida
Wannan hadin shi ake kira da 'kafata kafarki uwargida'.
Muddin kika lazimci wannan hadin a koda yaushe maigidanki zai cigaba da like miki. Saboda a koda yaushe zai jiki cikin ni'ima.
- Lemun zaki
- Madara peak
- Garin dabino
- Zuma
Yadda ake hadawa:
Zaki samun lemun zaki manya masu ruwa ki tace ruwan, kamar kofi uku ki juye, ki zuba madarar ruwa peak gwangwani biyu acikin ruwan lemun, sai ki zuba zuma dai-dai yadda kikeso, sannan kisa garin dabino kamar cokali uku. Idan kinaso zaki iya kara ruwa sai ki saka a fridge yayi sanyi, zai fi dadin sha.