Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye mukaminsa na shugaban hukumar Hisbah ta Kano

Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye mukaminsa na shugaban hukumar Hisbah ta Kano
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa 


A safiyar juma'a labari ya karade kafafen yada labarai cewa shugaban Hukumar Hisbah Malam Sheikh Aminu Ibrahim daurawa ya ajiye mukaminsa


Duba irin abubuwan da suke faruwa akan ayyukan da hukumar hisbah take yi karkarshin jagorancin Sheikh Aminu Ibrahim daurawa na operation dauka badala inda ake ta kamo samari mata da maza wanda hakan ake ganin ya saba da dokar kasa da take hakkin dan adam.


Babban kamun da yafi daga hankalin al’umma shine kama wata fitacciyar yar tiktok murja kunya wanda nan take hisbah ta kai ta kotu daga nan kuma aka samun labarin an anka sake ta, bayan korafi da yayi yawa sai aka bayar da sanarwar sake kama ta.


Sai dai bayanin gwamnan jihar kano engr Abba Kabir Yusuf, ya ja hankalin mutane wanda wasu ke ganin bai dace yai wannan furucin ba, wanda yace akwai Kurakurai akan ayyukan da hukumar hisbah keyi. 


Sai dai a safiyar juma'a labari ya karade kafafen yada labarai cewa shugaban Hukumar Hisbah Malam Sheikh Aminu Ibrahim daurawa ya ajiye mukaminsa. Inda yai Jawabi a wani faifan bidiyo. 


“Assalamu alaikum warahamatullah yau muna ashirin ga watan sha’aban 1445, wanda yazo daya ga watan march, 2024 ina daga nan jihar Kaduna inda muke gabatar da taro da yan majalisa karkashin sipika yadda za’a gabatar da doka wacce zata wajabta gwajin lafiya kafin aure a jihar kano kamar yadda sauraran jahohin Nijeriya suka yi irin wannan doka.


To dazu sai naji wasu jawabai suna ta fitowa daga jihar kano wadanda a gaskiya sun kashe min gwiwa, abinda nake ta kokari naga na gabatar a hisbah shine gyaran tarbiyya da gyaran hali, kuma nayi iya yina wajen gayyatar masu finafinai nayi zama da su, na basu shawarwari, munyi maganganu da yawa akan yadda za’a gyara tarbiyya al’umma ta yarda ake gabatar da fina finai Waɗanda suka saɓawa al’ada da addini da zamantakewar mu.


Haka na kira yan tiktok na dauki kudina cikin aljihuna da mataimakana muka haɗa muka basu kudin data da kudin mota muka zauna da su mukayi shawarwari, haka kuma na gayyato murja da yan uwanta masu yin tiktok mun zauna da su na basu shawarwari na yi musu nasiha ta hanyar da zasu bi su natsu su koma hayyacin su.


Daga baya wadanda basu ji ba suka koma suka cigaba da abubuwan da suke yi wanda yake taɓa tarbiya yake ɓata halaye kuma munyi iya ƙokarin mu don muga cewa munyi abinda ya kamata, to amma ina baiwa mai girma gwamna hakuri bisa fushi da yayi da maganganu da ya fada kuma ina rokon yayimin afuwa na sauka daga kan wannan mukami da ya bani na hisbah.


Kuma ina masa addu’a ina masa fatan alkhairi Allah ya bashi nasara Allah ya taimake shi ya taimaki gwamnatin sa, Allah ya daukaka addinin musulunci.


Wannan sune kalaman Kwamandan Hisbah na Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa. Shin yaya kuke kallon wannan jawabi na shehin malamin?


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post