Maganin Saurin Kawowa |
Abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima'i da yake aikatawa, ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima'i ne domin samun gamsuwa
Saurin kawowa itace babbar matsalar dake damun maza, maza da yawa basa iya haura minti biyar suna saduwa da iyalansu. Wani ma yace min yana saka azzakarinsa yake kawowa ba tare da daukar wani lokaci ba. Hakan yasa nai kokarin kawo muku hanyoyi magance matsalar.
Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa, wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka, don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:
Maganin Saurin Kawowa
a) Rage kosawa/kagara. Mai saurin inzali ya kamata ya cire tunanin jima'i daga kwakwalwarsa a lokacin da yake saduwa da iyalinsa. Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafın fara jima'i zai iya saka mutum "ya kone tun kafın ya tafasa". Masana sun nuna cewa bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima'i ba marar dadi a lokacin saduwa na karawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba.
Daukin jima'i baya biya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima'i da yake aikatawa, ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima'i ne domin samun gamsuwa wacce iyalinsa da yake sha'awa take biya masa. Kamata yayi tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima'i ne domin ya biyawa iyalinsa bukata farko kamin tasa. Abin lura, ka dauka ma cewa ba jima'i bane kake yi a lokacinda kake tarawa da iyalinka.
b) Don maganin saurin kawowa, A nemi kubewa danya (okra) guda 5, a wanke sa'annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi daya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa'annan a daura akan wuta a rufe tukunya. Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tace ruwan a kofin shayi, sai a zuba zuma ta bayar da dandano, a bari ya huce kadan amma asha da dumi. Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka. Kubewa nada sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa ga maza.
c) A nemi citta (ginger) musamman danya, a wanke a kuma karkare ta, sa'annan a dake ta, ayi shayi da ita, bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada dandano asha shayin da dumi. Ayi hakan safe da rana. Citta nada sinadari mai zafı na "gingerol" mai sanya yawan gudanar jini ga laura, wanda hakan na sanya karfın gaba da yin maganin saurin kawowa.
d) A nemi man na'a-na'a (peppermint oil) mai kyau, musammman dan Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan). A wanke gaba da ruwan dumi, a goge lemar sa'annan a shafa man ga zakari ya shiga fata, ga kai (glans) da tsawon sandar zakari (shaft), amma banda kofar fitsari (urethra). Musamman a shafa idan zakari yana mike, sai a jira bayan minti 10 zuwa 15 sa'annan a sadu da iyali. Man na'a-na'a na rage "sensitivity" na zakari, wato rage kaifın dandano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima'i. Haka kuma za'a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na'a-na'a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfın gaba da saurin kawowa.
e) Fita daga gaban mace na 'yan mintoci a lokacinda mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/penis grip) a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.
f) Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafın mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu. Don haka idan mutum yana son ya dade bai yi inzali ba to ya tari jima'i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafın yayi inzali.
g) Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist. Idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin daya daga cikin wadannan mutanen domin neman taimako. Akwai wasu hanyoyi da dama na magance matsalar.
Na tabbatar idan kuka yi amfani da wadannan hanyoyin na yin maganin saurin kawowa, zai taimaka muku wajen samun biyan bukata, tare da rage muku matsalar saurin inzali.