Lokutan Da Ake Karbar Addu'a |
Lokutan Da Ake Karbar Addu'a
Malamai sun bayyana lokuta da wurare da kuma halayen da ake karbar addu'a musulmi. Ina fatan duk wanda ya Karanta wannan rubutun zai taimaka ya turawa sauran yan uwa Musulmi.
Lokutan Karbar Addu'a
- Daren lailatul qadr
- Yankin dare na karshe
- Gurbin sallolin farilla
- Tsakanin kiran sallah da iqama
- Wata sa'a cikin kowane dare
- Lokacin saukar ruwan sama
- Lokacin da akeyin sahu don fita yaki domin Allah
- Wata sa'a cikin ranar juma'a. Ana rinjayar da wannan sa'ar da cewa daga sallar juma'a ne har zuwa bayan sallar la'asar.
- Lokacin shan ruwan zam-zam
- Yayin da ake yin sujada
- Lokacin farkawa daga bacci idan akayi addu'a
- Lokacin da ake yin addu'a kamar haka;" لا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ""La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin".
Tags:
Daga Malamai
Masha Allah
ReplyDelete