Kasashe 10 Da Aka Fi Dauke Wutar Lantarki A Afirka
![]() |
Kasashe 10 Da Aka Fi Dauke Wutar Lantarki A Afirka |
Dauke wutar lantarki a Najeriya a shekara ya fi yawan kwanakin shekara.
Wani rahoto kan kasashen da suka fi fama da matsalar wutar lantarki a duniya ya nuna cewa a Najeriya ana dauke wuta kusan sau 400 a shekara.
Rahoton da cibiyar Utility Bidder ta kasar Birtaniya ta fitar na nuni da cewa ana dauke wutar lantarki akalla sau 394 a duk shekara a Najeriya, wanda shi ne mafi muni a Afirka.
Hakan na nufin adadin dauke wutar da ake yi a kasar a duk shekara ya haura yawan kwanakin shekarar.
Cibiyar Utility Bidder wadda ke bincike kan dauke wutar lantarki da kuma asarar da hakan ke haifarwa a bangaren masana’antu ta bayyana cewa kasa ta biyu wajen dauke wuta a Afirka ita ce Afirka ta Tsakiya (CAR), amma na Najeriya ya zarce nata sau 46.
Ga dai jerin kasashen Afirka 10 da aka fi dauke wuta a Afirka da kuma adadin dauke wutarsu a shekara:
1. Najeriya – 394
2. Afirka ta tsakiya – 349
3. Benin – 336
4. Nijar – 264
5. Congo – 258
6. Gambia – 253
7. Burundi – 199
8. Zambia – 160
9. DR Congo – 148
10. Burkina Faso – 118
Binciken ya tataro alkaluma ne daga shekarar 2014 zuwa 2022, wanda ke nuna munin matsalar na iya shan bamban da hakikanin halin da ake ciki a halin yanzu.
Rashin tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya ya zame mata abin gori daga makwabtanta, musamman lokacin Gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON).
Leave Comments
Post a Comment