Karancin fetur ya kunno kai a Najeriya |
Kungiyar da ake wa lakabi da NARTO ta ce karya darajar Naira har sau biyu da gwamnatin Najeriya ta yi a kasa da shekera daya ya janyo wa mambobinta asarar da ba za ta iya ci gaba da daurewa ba
Kungiyar mamallaka manyan motocin da ake safarar man fetur a Najeriya da su na ci gaba da yajin aikin da ta fara a ranar Litinin, lamarin da ya fara haifar da karancin mai a wasu yankuna.
Kungiyar da ake wa lakabi da NARTO ta ce karya darajar Naira har sau biyu da gwamnatin Najeriya ta yi a kasa da shekera daya ya janyo wa mambobinta asarar da ba za ta iya ci gaba da daurewa ba. Tuni dai aka fara samun rahotannin dogayen layuka a gidajen mai na birnin Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya da ma babban birnin kasar Abuja.
A cikin wannan makon ne dai kungiyar kwadagon kasar ta bukaci 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwatarsu don yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu gagarumar zanga-zanga da ke adawa da tsadar rayuwa wacce ke ci gaba da bijire wa matakai dabam-dabam da mahukuntan na Abuja ke dauka.