Fatima Bintu Dadi kowa |
Fitacciyar jaruma a shirin Dadin Kowa Fatima Yakasai Ta Rasu
Allahu Akbar! Allah ya yi wa Fatima Yakasai (Bintu ta cikin shirin 'Daɗin Kowa' na Arewa 24 TV) rasuwa a ranar Lahadi.
Yan uwan marigayiya Bintu Dadin Kowa sun tabbatar wa da Freedom Radio rasuwarta, kuma ana sa ran za a yi jana’izarta a Kano a yammacin Lahadi.
Jama'a na ci gaba da bayyana alhinin su kan rasuwar jaruma Fatima, musamman abokan aikinta irin su Fauziyya D Sulaiman wacce ta bayyana rasuwar Fatima ta shirin Dadinkowa mai dogon Zango a matsayin babban rashi.
Muna addu’ar Allah ya gafarta mata amin.