Murja Ibrahim Kunya |
Hukumar Hisbah a Kano ta cafke fitacciyar Yar TikTok din nan Murja Ibrahim Kunya
Bayan nasiha da jan hankali, hukumar Hisbah a jihar Kano, ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya. Hakan ya biyo bayan kiraye-kirayen da al'umma suke yi kan irin yadda matashiyar ke wuce gona da iri.
Tun a kwanakin baya Hukumar Hisbah ta gayyaci Murja Ibrahim Kunya ita da sauran abokanta kan wani video da suka yi wanda suke yi kalaman batsa da ya saba da tarbiyyar musulunci.
Ko a karshen makon da ya gabata an ga Murja Kunya ita da abokanta cikin shigar rigar Nijeriya wanda ke nuna tsiraicinta.
Wasu dai na ganin daukar mataki mai karfi akan matashiyar shine abinda zai iya dakatar da abubuwan da take yi na badala a kafafen sada zumunta.