HOTUNA: Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Matashin Da Ya Auri Mata 3 A Rana Daya

HOTUNA: Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Matashin Da Ya Auri Mata 3 A Rana Daya

Hotunan matashin da ya auri mata 3

 

Al'umma Na Ci Gaba Da Taya Murna Ga Matashin Da Ya Auri Mata 3 A Rana Daya


 Sakonnin taya murna na ci gaba da bayyana ga matashi Tersugh Aondona wanda ya auri mata 3 a lokaci daya ranar Laraba a jihar Benue. 


Kamar yadda katin gayyatar bikin ya fara yawo a safiyar Laraba, an ga hoton angon shi da matan da ya aura su uku wanda aka bayyana sunayen su Blessing, Nancy da Sulumshima. 


An gudanar da shagalin bikin a babbar makarantar sakandare ta Jato-Aka, dake karamar Hukumar Kwande a jihar ta Benue. Kamar yadda shafin punch ya rawaito. 


An fara gudanar da bikin daga karfe 6 na yammacin ranar Laraba wanda aka wayi gari Alhamis. 

HOTUNA: Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Matashin Da Ya Auri Mata 3 A Rana Daya


Hotuna na ta yin yawo a shafukan social media kan yadda aka gudanar da bikin Tersugh Aondona da matan sa 3. Wani daga cikin abokan ango Akough Orduen ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook tare da taya murna ga abokinsa. 


HOTUNA: Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Matashin Da Ya Auri Mata 3 A Rana Daya

Ashe mutum yana iya auren mata har 3  lokaci guda ba tare da yin rikici a tsakanin su ba, musamman aure irin na gargajiya, wanna abin a yaba ne, cewar abokin ango Waalawa Mbaikyor. 


Lokacin da na fara ganin katin gayyatar bikin na dauka wasa ne na yi tunanin wasa ne, amma da na halarci wajen shagalin bikin na tabbatar da hakan kuma auren ya ban sha'awa, cewar Teryange Ephraim . 


Shin ya kuke ganin wannan auren, shin kuma ya baku sha'awa, kuma za ku iya auren mata 3 a lokaci guda? Ku bayyana mana ra'ayoyin a shashin comment 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. Nidai zan iyayi, Amma matan musulmai bazasu yadda auresu su ukku Rana daya ba.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post