Hotuna: Rijiyar Hudabiya Da Manzon Allah (SAW) Ya Nuna Mu'ujizarsa

Hotuna: Rijiyar Hudabiya Da Manzon Allah (SAW) Ya Nuna Mu'ujizarsa
Hotuna: Rijiyar Hudabiya Da Manzon Allah (SAW) Ya Nuna Mu'ujizarsa 


Wannan rijiya ta kasance wurin mu'ujizar da Manzon Allah (SAW) ya yi a lokacin zamansa a Hudabiya a shekara ta 6 bayan hijira.


Ruwa ya fito daga rijiyar Hudabiya

Manzon Allah (SAW) da Sahabbai sun yi sansani a Hudabiya na ’yan kwanaki a lokacin da ‘Yarjejeniyar Ridwan’ da Hudabiya Haka nan kuma a Hudabiya ne wasu mu’ujizozi suka faru a hannun Manzon Allah (SAW), wanda hakan ya kara wa yankin tarihi Mai muhimmanci.


Bara'a (رضي الله عنه) yana cewa: Sahabbai sun kai Dubu da Dari hudu a Hudabiya, kuma akwai rijiya daya tilo da ta kafe saboda yawan amfani da ita. Sai Manzon Allah (SAW) ya je bakin rijiyar ya yi tofi da Bakinsa Mai Albarka a cikinta. Nan take ruwa ya fara bulowa daga rijiyar, duk sahabbai sun sami isasshen ruwan da zai ishe su da dabbobinsu.


Ruwa ya fitowa daga yatsun Annabi (SAW).

Wata mu'ujiza kuma a Hudabiya, Jabir (رضي الله عنه) ya ruwaito. Ya ce mutane suna jin ƙishirwa a Hudabiya kuma Annabi (SAW) ne kaɗai ya sami ruwa a cikin bokiti.


Lokacin da ya fara alwala sai mutane suka kalle shi da tsananin sha'awar ruwan. Ganin sun zuba ido, sai Annabi (SAW) ya tambayi abin da ke faruwa? Da suka ba shi labarin cewa ba su da ruwan alwala ko kashe kishirwa, sai Annabi (SAW) ya sa hannunsa a cikin wannan bokitin, sai ruwa ya fara fitowa daga yatsunsa Mai Albarka. 


Jabir (رضي الله عنه) yana cewa a lokacin duk sun sami isasshen ruwan alwala da sha. Da wani ya tambayi Jabir (رضي الله عنه) ku nawa ne, sai ya ce: “ruwan zai iya isarmu ko da mun kai dubu dari. Duk da haka, mun kai Dubu Daya Da Dari Biyar a Wurin rijiyar.


A Yanzu An rufe rijiyar A Kusa wani wurin masana'antu kusa da Masjid al-Hudaibiah.


Na Samo Daga Tarihin Makkah Mukarramah Na Dr. Muhammad Ilyas Abdul Ghani, Na Fassara.





Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post