Janar Murtala Ramat Muhammad |
Hotuna: Motar Da A Ka Kashe Murtala Ramat Muhammad A Cikin Ta
A ranar 13 ga Fabrairu, 1976, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa ofishinsa da ke Barrack Dodan, Legas, wasu gungun sojoji sun yi wa motarsa kwanton bauna.
An harbe Murtala Muhammed mai shekaru 37 a duniya tare da mai taimaka masa a De-Camp (ADC), Laftanar Akintunde Akinsehinwa a cikin bakar Motar Mercedes Benz a wani yunkurin juyin mulkin da Laftanar Kanal Buka Suka Dimka ya jagoranta.
Bakar Motar Mercedes Benz Limo tana ajiye a gidan adana kayan tarihi na kasa da ke Legas. motar da ake kula da ita har yanzu tana da ramukan harsashi sama da 20 akan ta.
Motar shugaban da aka kashe na jan hankalin masu yawon bude ido 2000 duk wata.
Watakila motar ita ce motar da aka fi kula da ita a Najeriya a yau.