Yadda Ake Gane Mace Mai Son Abun Duniya |
Yawan sauraron Samari sabo da a ganinta yawan samarinta yawan abunda Zata samu a hannunsa. Ita mace mai son abin duniya bata iya rayuwa da namiji daya, kullum burinta ta hadu da Sabbin samari wanda za su biya mata bukatun ta.
Samari wannan darasi na yau naku ne, mun kawo muku wasu alamomi da za ku iya gane macen da kuke so bata son ku abin hannu ku kawai take so. Ina fatan duk wani saurayi zai dauki darasi daga abubuwan da zai Karanta daga abubuwan da za mu bayyana.
Yadda Ake Gane Mace Mai Son Abun Duniya
Ga jerin abubuwa ko alamomin da ake gane mace mai son abin duniya;
1) Yawan Baka labarin abun duniya, kai naga wata handset ta birgeni, naga wani less. Duk wani abu da kudi ne zai siya za ka samu tana yawan yi maka maganarsa. Ko kuma tace ka siya mata shi, ita batada wani tunanin da ya wuce ka siya mata ko kabata kudin ta siya.
2) Yawan Nuna sha'awar Duk abunda ta gani a wajen ka. Idan taji kamshin turare ko ta ganka da wani abu na birgewa za ta nuna sha'awar itama tana son ka siya mata.
3) Yawan tambayarka kayi mata abunda bai zama dole ba, ko tambayar kudi. Yana daga cikin yadda ake gane mace mai son abin duniya yawan rokon saurayi ya siya mata abu kamar anko, ko kayan sallah ko abin kwalam da Makulashe.
4) Yawan sauraron Samari sabo da a ganinta yawan samarinta yawan abunda Zata samu a hannunsa. Ita mace mai son abin duniya bata iya rayuwa da namiji daya, kullum burinta ta hadu da Sabbin samari wanda za su biya mata bukatun ta.
5) Yawan daukar abun kudi a gabanka tace ka biya mata. Idan Kana tare da ita da zarar ta ga wani abin da ya birgeta za ta nuna ka siya mata, wannan alama ce ta mace mai son abin duniya.
6) Hadin baki da kawaye. Tana iya hada baki da kawayenta don a cuce ka, ita mace mai son abin duniya burinta kawai ka kashe mata kudi, amma da zarar baka iya yi mata za ta yi kokarin rabuwa dakai.
Illolin Son Abun Duniya A Wurin Budurwa.
Duk da bayanin da mukai na yadda ake gane mace mai son abun duniya, akwai illoli da dama da hakan ke jawo wa ga matan dake yin hakan. Ga su kamar haka;
1) Samari zasu tsaneki. Duk macen da Samari suka gane son abin duniya ne da ita, zata rasa farin jini a wajen samari.
2) Da wuri ma'abota yaudara zasu yaudareki. Duk macen dake nuna kwadayi da son abin duniya wajen Samari babu shakka za'a kaita a barota.
3) Zaki fuskanci wulakanci a wurin mijin da kika aura idan har ya gane cewa don kudinsa kika aure shi.
4) Za'a yi miki kallon yar iska ko bakya iskanci. Ai ba ma sai an fada ba, domin duk macen mai son abin duniya kallon yar iska ake yi mata. Don babu saurayin da zai daukin kudinsa ya baki ba tare da ya nemi yin iskanci dake ba.
5) Yana bude hanyar yin iskanci. Duk wacce take da kwadayin son abun hannun saurayi yana jawo a yi iskanci da ita.
Shawara Ga Mata Masu Son Abin Duniya
Yafı kyau mace ta jure Duk Halin data Samu kanta, Duk abunda Yafı karfınki ki rabu dashi, karki mayar da saurayinki ATM dinki. Idan ya fuskanci ke ba mai son abin duniya bace shi da kansa zai dinga yi miki abubuwan da baki yi tsammani ba.