Hanyoyin Yadda Ake Gyaran Gashi
![]() |
Hanyoyin Yadda Ake Gyaran Gashi |
Yadda Ake Gyaran Gashi yai laushi da tsawo Musamman Don Mata
A Wannan darasi za mu kawo muku hanyoyin gyaran gashi na musamman wanda mata za su yi amfani dashi don gyara gashin kansu.
Gyaran Gashi Na Daya -(MAI TALIYA)
Wacce gashin kanta ke yawan karyewa, sai ta samu man dalbejiya ba tareda kin hada masa komai ba. Kullum da dare sai ki rinka shafawa. Yana hana zubar gashi kuma yanasa gashi yayi tsawo.
Gyaran Gashi Na Biyu -(AKORI ATTACHMENT)
Shima wannan hanya yana taimakawa wajen gyara gashi yai kyau. Ki samu
- Ganyen dalbejiya (bedi)
- Alovera
- Man zaitun
- Zuma
- Ruwan kwai
Ki samu danyen ganyen dalbejiya, bedi ki hada da alovera ki kirba shi sosai, sai ki saka zuma cokali uku, man zaitun cokali uku, ki zuba ruwan kwai aciki ki cakuda su ki shafa a kanki, ki samu leda ki rufe kan da ita. Amma da daddare zaki yi hakan da safe sai ki wanke gashinki sannan ki shafa man kwakwa da man ridi da na alayyadi. Wannan hadin zai sa gashinki yayi tsayi yayi kyau insha Allah.
Gyaran Gashi Na Uku -(ZARE HUTA)
Wannan hanya ce dake gyara gashi yai kyau da sheki. Ki samu
- Zaitu laus
- Man dinya
- Man alayyadi
- Man zaitun
- Man habbatus sauda
- Man dalbejiya
Sai ki hadesu guri guda ki rinka shafawa a kanki. Yana gyara gashi sosai yana kuma sashi yayi tsawo.
Gyaran Gashi Na Hudu -(ROBA HUTA)
Shima wannan hadin yana kara tsawon gashi da laushi, ki samu;
- Man kadanya
- Man zaitun
- Man habbatus sauda
Sai ki hadesu guri guda arinka kitso. Yanasa tsayin gashi sosai.
Leave Comments
Post a Comment