Hanyoyi Rabuwa Da Shaidanun Aljanu

Hanyoyi Rabuwa Da Shaidanun Aljanu
Hanyoyi Rabuwa Da Shaidanun Aljanu 



Wane Matakai Zan Bi Da Rabuwa Dasu, Sannan Wadanne Zan Bi Yadda Baza Su Dawo Ba? Koda Kuwa Sun Aure Nine Bisa Tsarin Musulunci.


Don rabuwa da matsalar shaidanu, farko anaso a sami wadannan mayukan kamar haka;

  • Man ridi
  • Man zaitun
  • Zuma
  • Man kwakwa
  • Garin habbatus saudah
  • Nikakken garin zaitun
  • Garin dabino
  • Turaren za afaran amma kadan


Sai a hadesu guri guda a dama da zuma lita daya (1 litre sannan sai ayi alwala a karanta wadannan ayoyin a tofa aciki:


- سورة الفاتحة 7

-103-102 خَوَاتِمُ سُورَةُ الْبَقَرَةِ

سورَةُ الْأَعْرَافِ آية 56-54

خَوَاتِمُ سُورَةُ الْإِسْرَاءِ

سُورَةُ يُونُسَ آية 81

- سُورَةُ الْأَنْبِيَاءِ آية 17

سُورَةُ الْفُرْقَانِ آية 23-22

سُورَةُ الْصَّافَّاتِ آية 10-1

سورَةُ الرَّحْمَانُ آية 36-33

- سُورَةُ الْجِنَّ آية 7-1

- خَوَاتِمُ سُورَةُ الْحَشَرِ

- سُورَةُ الْبُرُوج كلها

- سُورَةُ الْفَلَقِ

- سُورَةُ النَّاسِ


- Suratul fatiha x7

Suratul Baqarah ayata 1-7

- Suratul Baqarah ayata 102-103

- Amanar Rasul

الدة الأعراف آية 6

-Suratul A'araf ayata 54-56

الد سورة الإسراء

- Karshen suratul Isra'i

يوشين اية 81

Suratu Yunus ayata 81

7 البناء آية

Suratul Anbiya'i ayata 17

الفرقان آية -3

Suratul Furqan ayata 22-23

الرحمان اية

Suratus Saffat ayata 1-10

Suratur Rahman ayata 33-34

العناية ٦-١

- Suratul Jin ayata 1-7

سورة الحشر

- Karshen suratul Hasher

الزوج كلها

- Suratul Buruj dukanta

- Suratul falaq

اكل

- Suratun Nas


Wadannan ayoyi su za'a karanta ko wacce kafa hakwaj (7) a tofa acikin wannan hadin. Anason mara lafiya kullum da safe in ya tashi yasha cokali biyu bayan yaci abinci, haka da daddare in zai kwanta. Sannan a sami man alayyadi da man ridi da man kwakwa da muskil aswad (wato bakin muski), ayi masa rukiyya na wadannan ayoyin a tofa aciki. Me matsalan jinnu sai ta rinka shafawa daga goshinta zuwa bayan kanta, kirjinta zuwa cibiyarta, da kuma kasan mararta. Sannan anaso a karanta wadannan addu'o'in suma a karanta a tofa acikin ruwa mai ganyen magarya aciki, sannan a diga bakin miski a ruwan. Sai arinka fesa masa ajikinsa kuma arinka bashi ruwan yan asha da safe da kuma da daddare.


Hadin Turare Na Mara Lafiya

Ku samu wadannan abubuwa kamar haka;

  • habbatus sauda
  • Khustil hindil bahri
  • Hantit
  • Ganyen tsamiya
  • Ganyen magarya

Hadin mayukan da akayi wannan karatu wanda ake shafawa, sai a zuba su kadan acikin wannan hadin, sai mara lafiya ya rinka turare jikinsa dashi. Insha Allah ko jinnun sihirine zai rabu dashi har abada.


Jinnul Ashiq 

Aljanin dake auren mata. Wanda aljani ya aureta har ya kasance ta rasa mijin aure ko kuma ta kasa zaman lafrya da mijinta, kullum cikin fada da tashin hankali. Ko ya saka mata tsanar mijinta ko 'yan uwanta koma 'ya'yanta.


Zata samu muskil-aswad wato bakin muski ko muskil- kaabah wato miski mai hoton ka'abah ajiki. Zata karanta wadannan ayoyi aciki kamar haka;


a diga bulkume

- آيةُ الْكُرْسِيُّ

سورَةُ الْكَهْفِ آية 10-1

- خَوَاتِمُ سُورَةُ الْمُؤْمِنون

سُورَةُ الصَّافَاتِ آية 10-1

- سُورَةُ الْمُلِكِ

- سُورَةُ الْجِنَّ

- سُورَةُ الْبُرُوج

- Ayatul kursiyyu

- Suratul kahfi ayata 1-10

- Karshen suratul mu'minun

- Suratus saffat ayata 1-10

Suratul mulk

Suratul Jinn

Suratul buruj

Suratul ikhlas

- Suratul falaq

- Suratun nas

Zata hada ta rinka shafa shi a kasan mararta da kirjinta idan zata kwanta. Sannan ta tabbatar da tana kwana da alwala. Kuma ta cire duk wasu hotuna dake cikin dakinta sannan ta karanta li'ilafi akowace kusurwa, ta tofa kuma ta shafe jikinta da yawunta. Sai ta karanta wannan addu'ar kamar haka;


"اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِن سُوءِ أَحلام وَ اسْتَجِرُكَ مِن تَلاعِبِ الشَّيْطَانِ فِي


الْيَقْظَةِ وَالْمَنَامِ"


"Allahumma inni a'uzhubika min su'i ahlam, wa astajiruka min tala'ibush shaidanu fil yaqzati wal manami". Ko kuma ki karanta Suratul Sajda.


Koda ya kasance idan kin samu juna biyu kina 'barinsu sakamakon jinnu, to idan kika karanta wannan addu'ar kin rabu dasu har abada da izinin Allah.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post