Hadin Maganin Gyaran Jiki Don Mata
![]() |
Hadin Maganin Gyaran Jiki Don Mata |
Yadda ake hada maganin gyaran jiki da rage kiba da magance Nankarwa
Kina so ki zama 'yar caras-caras? sawai-sawai? to sai ki rage tumbi da kibarki, sai ki koma cas-cas dake ki hadu. Samu wannan abubuwan;
- Lipton
- Raihan (daddoya)
- Naskafi (Nescafe)
- Lubban zakar
- Sugar
- Kanunfari
- Lemun tsami
Ki hada wadannan kayan hadin ki rinka shayi dasu a kullum safe da yamma. Insha Allahu zakiga yadda zaki koma, 'yar sawai-sawai ki goge, kuruciyarki ta fito, sai mijinki ya kalle ki vaji dadi.
Rage Kiba
Matan dake son rage kibarsu suna iya bin wannan hanyoyin kamar haka;
- Danyar citta
- Kanunfari
- Na'a-na'a
- Tuffa (ruwan jan apple)
Sai ki hadasu guri guda a tafasa. Duk lokacin da aka gama cin abinci sai asha shi da zafin shi. Za'a iya saka zuma kadan.
Maganin Nankarwa (STRETCH MARKS)
Nankarwa shine irin wannan zanen da yake fitowa acikin mace, da zarar ta fara haihuwa ko kuma in tayi kiba. Yakan fito a cikin mace ya sanya fatar cikin duk ta yamutse.
(1) Ana amfani da man dodon kodi a shafa a ciki. Yana gyara fatar ciki ta koma kamar ba'a haihu ba. Sannan a samu sabulun sa (duk ana samu a islamic chemist) a rinka wanka dashi.
(2) Man kadanya Man zaitun Lemun tsami.
Ki hada man kadanya da man zaitun guri guda, sai ki matse lemun tsami akai, amma bada yawa ba. Ki motsa sosai sannan sai ki rinka sharewa. Ki yawaita yi Insha Allahu zata goge.
(3) Ana shafa zuma da kwalli da ganyen bedi da daddare in zaki kwanta bacci, sannan da safe ki samu ruwan dumi ki wanke.
Karin Kiba ('YAR DUM-DUM)
Matan dake bukatar su kara kiba jiki su yi wannan hadin kamar haka;
- 'Ya'yan hulba
- Alkama
- Waken suya
- Gyada
- Garin dabino
- Garin farar shinkafa
- Madara
- Zuma
Zaki samu alkama da farar shinkafarki ki jika. Sai sun kwana sai ki shanyasu su bushe, sannan ki kai anuka. Shima waken suyar da hulba ki maida su gari. Sai ki sami garin dabino, gyada ma a soya ta sama-sama sai anuka ta. Sai ki hada garukan waje guda, sannan ki debi cokali biyu (2) ki zuba a ruwa rabin kofi, ki dora a wuta har ya tafasa. Sai ki sauke kisa madara ta ruwa ko ta gari da zuma ki hada kisha, musamman idan zaki kwanta bacci. Cikin dan kankanin lokaci zaki zama 'yar lukuta da yardar Allah.
Leave Comments
Post a Comment