Hadin Karin Niima Don Ango Da Amarya |
HADIN IDON ZAKARA (MAI TUBALI)
Karin sha'awa da ni'ima ga amarya da ango. Sabbin Ma'aurata da suka yi aure da wadanda ke shirin yin aure wannan hadine zai taimaka muku wajen tabbatar da karin niima.
Domin yin wannan hadin ku samu wannan abubuwan kamar haka;
- Zuma
- Idon zakara 'danyensa
A daka idon zakara yayi lukwi, sannan a kwaba da zuma sai mace tayi matsi dashi a gabanta, bayan kamar awa daya sai ta wanke.
Hadin Kabewa (SARKAR MATA)
Hadine wanda mace da namiji duk suna amfani dashi, domin kara sha'awa da ni'ima tare da zumburar da sha'awarka nan take.
- Madara ta ruwa
- Danyar kabewa
- Zuma
Ana dafa kabewa, amma kada a barta ta dahu sosai, sai a markada ta a zuba madara ta ruwa da zuma a sha.
Hadin Ruwan Dabino (MAI DABAI-BAYI)
- Zumburar da mace.
- Dabino
- Garin minannas
- Madara ta ruwa
Zaki bare dabinonki dai-dai yadda kikeso, sai ki jika ki cire 'ya'yan ciki. Sai ki markada a blender ki ajiye acikin fridge. Duk lokacin da zaki sha ki debi cokali daya, idan yayi kauri ki kara ruwa kadan.
Hadin Citta (RAKUMI DA AKALA)
- Kanunfari
- Citta mai kyau
- Zuma
Ki samu robar swan ko makamancinta ki zuba kanunfari aciki, ki samu citta mai kyau ki zuba aciki. Idan ya kwanta sai ki tsiyaye ruwan kisa zuma ki rinka sha.
Hadin Danyar Gyada (ZAMAN GIDA)
Wannan hadin mace da namiji duk suna amfani dashi. Domin yana kara ni'ima harma yasa uwar gida tacewa miji tashi in goyaka.
- Alkama
- Danyar gyada
- Waken suya
- Aya
- Madara ta ruwa
Ki samu danyar gyada da alkama kofi daya, aya kofi daya, waken suya kofi daya. Sai ki jika ki markada ki tace. Idan yazama gasara sai ki rinka damawa kamar yadda ake dama koko, ki zuba madara ta ruwa kiyi kamar sati biyu kina yi.
Hadin Habbatussauda (KORE MIJIN ALJAN)
Wannan hadin yana sa sha'awa da kara ni'ima ga mace harma ya kara kareta daga mazajen aljanu. Har yasa sha'awarta ta karu fiye da sadda take da lafiyarta.
- Garin habbatus sauda
- Albabunaj
Ki tafasa garin habbatus sauda da albabunaj ki rinka sha. Kina iya kama ruwa da shi sannan ki turara gabanki dashi.
Hadin Hulba (TAURARUWA)
- Gyada
- Aya
- Mazarkwaila
- Hulba
- Nono ko madara
ki sami gyada rabin kwano, aya rabin kwano, mazarkwaila faifai daya. Ki soya gyadar sama-sama sai ki daka (amma kada ki barta tayi mai). Itama ayar haka zaki yi, sai kin wanke ki cire dattin cikinta da tsakuwar sai ki soya sama-sama sannan ki daka.
Itama mazarkwailan dakata zakiyi, amma kada ki barta ta dunkule garinta ake so. Sai ki hade su guri guda ki zuba hulba cokali daya, sai ki samu mazubi mai kyau ki zuba aciki. A rinka sha da nono ko madara. Zaki sha mamaki.