Hadin Karin Ni'ima Da Ridi Don Uwargida Da Amarya |
Hadin Karin Ni'ima Da Ridi Don Matan Aure
Ana so miji da mata su rinka amfani da wannan hadin domin karin ni'ima, ya kuma sa koda yaushe ta rika bukatar mijinta kusa da ita. Don’t yin wannan hadin za ki samu wadannan abubuwa kamar haka;
- Rawan kwakwa
- Madara peak
- Zuma
- Ridi
Za ki hadesu guri guda ki rinka sha. Yana kara ni'ima sosai da sosai. Sannan kuma yana kara dumi da damshin farji.
Wani Hadin Ridin (KARIN NI'IMA DA KUZARI)
Ana so miji da mata su rinka sha domin motsa sha'awa. Za Ku samu wadannan abubuwa kamar haka;
- Kanunfari
- Zuma
- Garin ridi
- Nonon shanu mara tsami
Ki dafa kanunfari da ruwan zafi, idan ya dauko nuna(dahuwa) sai ki sauke ki sami garin ridi da nonon shanu mara tsami, ki hade guri guda ki gauraye. ki saka a fridge ko ki saka kankara idan yayi sanyi kisha.
Wannan hadin idan kika yi sai kuma bayan mako daya za'a kuma yi.