Gyaran Nono, girman nono, manyan nono |
Sirrin Gyaran Nono, Girman Nono, Cikowar Nono, Manyan Nono da Hadin Gyaran Mama
Wannan hadin yana karawa mace girman nono kuma ya hana shi faduwa. Koda ace mace tana shayarwa idan har tana amfani da wannan hadin tofa alasan barka domin kuwa za ta yi mamakin yadda za ta kasance.
Gyaran Nono Na Daya 1
Domin yin wannan hadin na gyaran nono ku samu wadannan abubuwa kamar haka;
- Farar shinkafa
- Garin alkama
- Garin habbatus sauda
- Garin ayaba (plantain)
- Gyada mai malfa (mai zabo)
- Aya
- Madara
- Zuma
Zaki shanya plantain bayan kin soya shi sama-sama ya bushe, sai ki daka ki hada da garin alkama da garin shinkafa. Sai ki hada aya da gyada a markada a tace ruwan, ki dora akan wuta a zuba garikan da aka ambata a sama, a zuba madara ta gari da zuma ki dama yayi kauri.
Wannan hadin shi zaki rinka sha safe da yamma, zaki yi wannan hadin kafin sati biyu da yin yaye. Kuma wacce ma bata shayarwa zata iya yi, sai ki nemi rigar nono acuci maza ki saka, sannan ki samu garin hulba ki rinka sa nonon da ita.
Gyaran Nono Na Biyu 2 (MAI TOLO)
Shi kuma wannan hadin gyaran nono ne da ake yin sa da kunun alkama da madara zaki yi shi sau biyu a rana, zaki yi hakan kafin sati biyu ayi yaye, da kuma sati biyu bayan yaye.
Gyaran Nono Na Uku 3 (BAKANDAMIYA)
Hulba za a samu a tafasa ki rinka gasa nonon dashi, sai kuma a shafa man hulba za'a ga abin mamaki.
Gyaran Nono Na Hudu 4 (MAI LUDAYI)
A tafasa hulba a gasa nono, sai a shafa kwan salwa, a kuma fasa kwan salwan guda uku a sha.
Wannan hanyoyi ne na gyara nono wanda kesa taimakawa wajen girman nono, tsayuwar nono, cikowar nono, manyan nono, duk wace ke son Taylor gyara nono ta yi amfani da wannan hanyoyin da muka bayyana.