Hadin Gyaran Jikin Amare (Saka Laushin Fata) - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Hadin Gyaran Jikin Amare (Saka Laushin Fata)

Hadin Gyaran Jikin Amare (Saka Laushin Fata)
Hadin Gyaran Jikin Amare (Saka Laushin Fata) 



Gyaran jiki na mata musamman wanda suke yawan yin aikin gida 


Wannan hanya ce da mata za su bi ko amare ko wadanda suka yi auren don gyaran jikinsu. Zai taimaka jikinki ya kasance koda yaushe a cikin laushi musamman hannu. 


Kullum bayan kin gama aiki, ki hada man zaitun da gishiri kadan ki rinka shafawa sau daya ko sau biyu a rana.


Ki hada sugar da butter dai-dai misali ki rinka murzawa a hannunki yayi tsawon misalin mintuna goma.


Ki hada gilasirin (glycerin) da turaren miski da lemun zaki ki rinka shafawa a hannunki ko wane dare.


Ki matsa ruwan lemun tsami da man zaitun ki rinka shafawa a hannunki, zai dawwama da taushi.


Ki samu tumatir kwaya bakwai ki matse ruwan ki hada da man zaitun cokali daya ki rinka shafawa kullum.


Da yawa daga cikin mata ba kowace mace bace tasan cewar idan ta gama wanke-wanke ta samu ruwan dumi ta wanke hannunta sannan ta shafe shi da mai. Duk matar da take hakan batada matsala ta fannin bushewar tafin hannunta.


Cikin wadannan abubuwan da muka kawo, duk wanda kika dauka zai miki amfani da yardar Allah.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel