Hadin Furen Zogale (TASKA) Don Maza Masu Aure |
Hadin furen zogale dake rikitar da namiji a yayin Jima'i
Wannan hadin ana so namiji ya rinka amfani dashi, domin karin ni'ima da kuzari. Hadin zai sa namiji ya kasance koda yaushe zai bukaci mace kusa dashi.
Don yin wannan hadin ana samun wadannan abubuwan kamar haka;
- Ganyen zogale
- 'Ya'yan zogale
- Dabino
- Cukwi
A shanya furen zogale da 'ya'yan zogale acikin inuwa. Sai a hada da dabino a daka a rinka sha da nono, ko madarar ruwa. Wannan hadin yana saurin sauko da ni'ima.
Hadin 'Ya'yan Zogale
Wannan hadin shi ake cewa karya gado. Yana kara karfi da nishadi da dadin jima’i, za'a samu wadannan abubuwan kamar haka;
- 'Ya'yan zogale
- Mazarkwaila
- Cukwi
- Kantu (ridi)
- Farar shinkafa
- Danyar gyada
Yadda Ake Hadin 'Ya'yan Zogale
Zaki wanke farar shinkafarki, sai ki dan soya ta sama- sama, ma'ana kada ta soyu kwarai. Zaki tafasa ruwa sai ki zuba gyada. Kiyi sauri ki tace ta sai ki shanya. Idan kinyi daidai zakiga bawon gyadar yana cirewa dakansa kafin ta bushe.
ldan tayi sai ki murmusheta ki dake lukui, ki daka cukwi da dabino, ki cire 'ya'yan zogale ki cire kwafsar ki cire fatar sannan ki shanya a cikin inuwa. Idan ya bushe ki hadesu da dakakkiyar soyayyar shinkafarki da gyada da dabino. Sai ki rinka sha da madara ta ruwa.
Hadin Gwanda
Wannan hadin shi ake cewa 'sa kishiya tagumi'. Idan kuma ke daya ce tofa sai dai a kirashi 'mutu ka raba'. Za ki samu wadannan abubuwa:
- Kankana
- Gwanda
- Dabino
- Zuma
Zaki samu kankana ki gyarata a jika dabino, sai a hade su guri daya a markada su, a zuba zuma a ciki a rinka sha.