Don Matan Aure: Hadin Saka Kishiya Tagumi

Wannan hadin yana sanya maigida ya kasance a dakinki koda yaushe

Wannan hadin yana sanya maigida ya kasance a dakinki koda yaushe. Idan ma kinada kishiya har sai ta rasa me yake idan ya shigo dakin naki.


Wannan hadin yana sauko wa mace ni'ima. Maigida zaiji baya gajiya da kai miki ziyara. Idan kina son kiyi wannan hadin zaki samu wadannan abubuwan;


  • Kwakwa
  • Garin dabino
  • Madara peak

Yadda ake hadawa:

Ki markada kwakwa da dabino ki tace, sai ki zuba madarar peak ki rinka sha. Zakiga abin mamaki Insha Allah.


Hadin Kaza 

Wannan hadin na mata da maza ne. Yana sanya ma'aurata farin ciki duk lokacin da suka sadu da juna. Ki samu;

  • Kaza
  • Saiwar malmo

Yadda ake hadawa:

Zaki samu saiwar malmo ki dafa shi, sai ki tace ruwan. Ki samu kazarki ki gyarata, ki hada mata komai na dahuwa. Sai ki zuba ruwan dahuwar malmon da kika tace aciki. A jaraba za'aga biyan bukata da yardar Allah.

Hadin Danyar Gyada 

Wannan hadin yana sanya maigida ya kasance a dakinki koda yaushe. Idan ma kinada kishiya har sai ta rasa me yake idan ya shigo dakin naki.


Ki samu danyar gyada ki wanke ta, sai ki jika ta ki kai a markada maki ki tace. kya iya zuba sugar ko zuma sai ki saka a fridge, domin gudun lalacewa. In zaki kwanta kisha karamin kofi. ki sha mamaki.


Manta Wayarka

Wannan hadin shima yanada matukar amfani ga jikin mace. Ki samu:

  • Ruwan rake
  • Ruwan kankana
  • Madara

Yadda ake hadawa:

Ki hadasu waje guda ki motse ki rinka sha sau uku a yini. Ki jaraba da akwai amfani acikin wannan hadin


Makale Mata 

Shima wannan hadin yana da tasiri sosai domin yana kara ni'ima ga mace. Ki samu wannan abubuwan;

  • Aya
  • Waken suya
  • Kwakwa
  • Dabino
  • Madarar rúwa
  • Zuma

Yadda ake hadawa:

Ki hadesu guri guda ki markade, sai ki tace ki zuba zuma da madarar ruwa ki rinka sha. Keda kanki zakiji canji tun daga lokacin da kika fara sha.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post