Sirrin mata
Don Mata: Hadin Gyaran Fuska
Friday, February 23, 2024
0
Don Mata: Hadin Gyaran Fuska |
Salon gyaran jiki da fuska don mata musamman Amare
Hanyoyin gyaran fuska tayi sumul tayi haske, kurajen fuska su fita. Ki samu;
- Tumatur
- Madara peak
Ki hadesu guri guda ki kwaba dai dai gwargwadon yanda zai isheki, sai ki shafa a fuskarki ya samu tsayin mintuna talatin akan fuskar naki sai ki wanke. Wannan yana gyara fuska sosai.
Gyaran Fuska Na Biyu (WANNAN HAR KANANAN TABO YAKE CIREWA)
Ki samu wannan abubuwan;
- Lemun tsami
- Zuma
- Kwai
Ki samu zuma sai ki matse lemun tsami a cikinta, sai ki saka kwai ki rinka shafawa a fuska, ki samu kamar tsayin mintina ashirin, sai ki shafa zaitu laus bayan kin wanke ta.
Gyaran Fuska Na Uku ('YAR LUMUS)
Ki samu tumatir nunanne ki kwashe 'ya'yan ciki ki zubar, sai ki rinka gogawa a fuskarki kafin ki shiga wanka. In kin fito ki shafa man ridi dana hulba.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment