Domin Neman Karin Ni'ima (Mai Suna Linzamina)
Domin Neman Karin Ni'ima (Mai Suna Linzamina) |
Hanyoyin hadin Karin niima da dandano a zamantakewar aure
Irin wannan hadin shine ake kira da 'Linzamina'. Yana matukar saurin kawowa mace ni'ima. Idan za kiyi wannan hadin za ki nemi wadannan abubuwan kamar haka;
Zogale
Zuma
Nono
Yadda ake hadawa (karin niima)
ki busar da zogalenki amma ba a cikin rana ba, sai ki daka shi yayi laushi sosai. Zaki iya tankadewa, sai ki rinka dibar cokali daya kina zubawa a nono, ki zuba zuma cokali uku aciki ki rinka sha. Wannan hadin yana matukar karawa mace ni'ima da lafiya səsai.
Hadin Karin Ni'ima Na Bita Zai-Zai
Wannan hadin shi ake kira da 'bita zai-zai'. Sirrine wanda yake kawowa mace ni'ima, koda ace irin matan nan ne wadanda basuda ni'ima. Yana karawa mace dadi, idan, maigida ya sadu da ita ya rude. Ki samu wadannan kayan hadin;
- Bawon kankana
- Saiwar zogale
- Kanunfari
- Mazarkwaila
- Zuma
Yadda ake hadawa:
Zaki hadasu guri guda ki tafasa su, in sun dahu sai ki tace ruwan ki mayar da ruwan acikin tukunya, sai ki zuba mazarkwaila da kanunfari. Idan ya samu 'yan mintoci sai ki sauke ki rinka sha. Zakiji ki kinyi fanjam da nuwa(ruwan ni'ima) da yardar Allah.
Kafata Kafar Ki Uwargida (Hadin Karin Ni'ima)
Wannan hadin shi ake kira da 'kafata kafarki uwargida'.
Muddin kika lazimci wannan hadin a koda yaushe maigidanki zai cigaba da like miki. Saboda akoda yaushe zai jiki cikin ni'ima. Samu wannan kayan hadin;
- Lemun zaki
- Madara peak
- Garin dabino
- Zuma
Yadda ake hadawa:
Zaki samun lemun zaki manya masu ruwa ki tace ruwan, kamar kofi uku ki juye, ki zuba madarar ruwa peak gwangwani biyu acikin ruwan lemun, sai ki zuba zuma dai-dai yadda kikeso, sannan kisa garin dabino kamar cokali uku. Idan kinaso zaki iya kara ruwa sai ki saka a fridge yayi sanyi, zai fi dadin sha.
Leave Comments
Post a Comment