Canjin Naira Da Wasu Kudaden Waje A Ranar 26 Ga Watan Satumba 1983. |
A lokacin Naira tafi Dalar Amurka daraja. Domin a kasuwar canji da Naira daya za a baka Dala 1 da Centi 50 da Anini (Penny) 25.
Ga yadda canjin Naira da wasu kudaden kasashen waje suke a ranar 26 ga watan Satumba 1983.
A Lokacin Najeriya ta fara shiga matsalar tattalin Arziki kenan
Ya na daya daga cikin dalilan da ya sa Sojoji sukayi juyin Mulki a ranar 31 ga watan Disamban 1983, wanda ya kawo gwamnatin Janar Muhammadu Buhari.
A lokacin Naira tafi Dalar Amurka daraja. Domin a kasuwar canji da Naira daya za a baka Dala 1 da Centi 50 da Anini (Penny) 25.
Deutsche mark na jamus 4 ne yake a matsayin Naira daya. A zamanin kudin Franc na kasar Faransa 14 da yan mutsamutsai ne yake yin Naira Guda.
Sannan darajar Pounds 💷 na Ingila, su na kankankan da Naira.
Yen 💴 na kasar Japan kuwa 366 ne yake yin Naira daya.
Sannan Malam wa yake maganar takardar Yen ta kasar China? ko kusa ba wanda yake Maganarta domin Naira ba sa'arta bace.