Bayan kamun da Hisbah sukai mata kotu ta aike da princess Ramlat gidan yari

Bayan kamun da Hisbah sukai mata kotu ta aike da princess Ramlat gidan yari
Ramalat princess

Takardar karar ta bayyana cewa an sami jarumar Tiktok din tana yin amfani da kafar sada zumunta tana yin kalaman badala.


A daren Juma’a ne Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa na kotun Musuluncin da ke unguwar Sharada ya sa ajiye Ramlat a gidan yari bayan Hukumar Hisbah ta gurfanar da ita.


A kwanakin nan ne wani bidiyon Ramlat ya karade soshiyal midiya, wanda a ciki take tallata madigo, har ta bayyana kanta a matsayin mai wannan muguwar dabi’ar.


A cikin bidiyon, an ji matashiyar na cewa, duk wanda ke son zai aure ta, to dole sai ya amince cewa ita za ta auro tata matar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.


Takardar karar ta bayyana cewa an sami jarumar Tiktok din tana yin amfani da kafar sada zumunta tana yin kalaman badala.


A cewar takardar kara laifukan da ake zargin ta da su laifuka ne da suka saba da sashe na 341 da 275 da 227 na Kundin Pinal Kod.


Wacce ake zargin ta amsa laifukan inda ta nemi afuwar kotu bisa laifukan da ta aikata. Sai dai saboda kurewar lokaci kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 19 ga Fabrairu don yanke hukunci.


Haka kuma kotun ta yi umarnin tisa keyar Ramla zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a sake dawowa gaban kotun.


Wannan na zuwa ne bayan wata kotun Musulinci a jihar ta yanke hukuncin daurin wata shida kan laifin badala ga wani mai suna Murtala Adamu, wanda aka kama tare da fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.


An yanke masa hukuncin ne washegarin da kotun ta sa a tsare Murja a gidan yari kan laifin badala da koyar da karuwanci.


An gurfanar da Murja ne bayan an kama su da Murtala Adamu a unguwar Hotoro, bayan jami’an Hukumar Hisbah sun kai samame sakamakon korafin da mazaunar unguwar suka shigar.


Murja dai ta musanta zargin da ake mata na koyar da karuwanci, badala, da kuma tayar da hankali jama’a.


Kotun dai ta yanke alakar Murtala da Murja Kunya da cewa ba shi ba ita, sannan ta haramta masa zuwa unguwar tsawon shekaru biyu, kuma muddin aka gan shi zai dandana kudarsa.


Aminiya ta ruwaito cewa, an kuma ba wai Murtala Adamu takardar kulla yarjejeniya wadda ya cike kuma ya sanya hannu.


Kotun da ke unguwar Gama ta bai wa matashin zabin biyan tarar N30,000 kan laifin tayar da haniya da aikata badala.


Shin yaya kuke ganin wannan ayyukan da Hukumar Hisbah ke yi, sannan kuna ganin hukuncin da kotu ta yi ya yi daidai? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post