Amfanin 'ya'yan itatuwan gargajiya ga dan adam |
Sirrin amfanin goriba, aduwa, magarya ga Dan Adam
Cin kayan itatuwa na gargajiya irinsu magarya, aduwa, kurna, goriba da giginya, da sauransu, na da matukar amfani ga jikin dan Adam.
Kamar ita goriba, tana da amfani sosai, domin akwai dusa a cikinta, da ake kira 'fibre' a turance. Ita dusar nan, tana taimaka wa masu fama da basir wato 'pile' a turance, da kuma masu kiba, saboda cika ciki da take, sannan kuma ta kunshi sinadiran 'phosphorus, da 'vitamin C', saboda wannan tsami-tsamin da dan sikarin da ke ciki, da yake taimakawa.
Sannan kuma akwai 'magnesium', wato dai sinadirai ne masu taimaka wa jikin dan Adam. Akwai sinadirai da ake kira 'co-N da co-factor', masu taimakawa a irin abincin da muke ci, na jini, kamar su protein, carbohydrate. To suna taimaka wa wadancan abubuwan, don gyaran jiki da kara lafiya. Wato duk 'ya'yan itatuwan da suke da ganye, ko suke da dandano na 'ya'yan itace mai 'ya'ya, to akwai wasu sinadirai da suke da shi, na 'vitamin A, vitamin B, vitamin K', da kuma wasu sinadirai na wannan magnesium din da phosphorus din, da suka kunshi gyaran jiki, da gyaran fata, da kuma kariya daga kamuwa daga cututtuka, musamman na daji wato 'cancer'.
Duk wadannan kayan itacen suna taimakawa. Sannan musamman masu ciwon suga, wato 'diabetes' da hawan jini, goriba da aduwa da kurna da gawasa na taimaka musu sosai, musamman idan aka ci, tare da dusar ciki, suna sauko da sugar sosai, ga masu ciwon suga. Don haka duk wadannan kayan itatuwan suna da mahimmanci sosai, kuma akwai abin da za ka samu daban, a kowane dan itace da babu a wani, shi yasa duk suke da amfani baki daya ga jikin dan Adam.