Amfanin Cin Kwai A Jikin Dan Adam

Amfanin Cin Kwai A Jikin Dan Adam
Amfanin Cin Kwai


kwai yana da amfani wajen rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya. 


Kwai wani sinadari ne da kaza keyi wanda yake da matukar amfani a jikin dan adam wanda yake kunshe da abubuwa kamar haka vitamin a, vitamin k, vitamin d, vitamin b6. Sannan kuma yana kunshe da calcium a cikinsa wanda yana matukar kara karfin kashi, karfin hakora a jikin dan adam. Haka kuma kwai yana dauke da zinc wanda yake taka rawar gani a jikiin dan adam.


Amfanin shan danyen kwai ga maza da kuma amfanin shan danyen kwai ga mace duka yana tasiri a jikin su tare da bayar da gudunmawa wajen inganta lafiya. kwai yana da amfani wajen rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya. Sannan amfani da kwai na taimakawa wajen hana kamuwada hawan jini. 


Gameda fadar mutane da yada jita jita na cewa wai ko kwai nawa kaci kamar kaci kwai 10 kwara 1/ zai yimaka amfani a jikinka to wannan ba gaskiyabane ko kwai talatin kaci to 30/ dinan za su yimaka aiki yanda yaimata ajikinka. 

 

Amfanin kwai ga mata / Amfanin kwai ga maza

Kamar yadda na fada tun a farko kwai yana da amfani sosai ta hanyoyi da dama, wani bincike ya ce danyen kwai yana kara kiba, hadin danyen kwai don yin magani da sauransu. Ga wasu daga cikin karin amfanin danyen kwai. 


1) Yana da kyau macce mai juna 2 ta rika cin kwai don yana taimakata a jikinta, wannan amfanin kwai ga mata Kenan 

2) Ana so masu diabetes su rika cin kwai don yana kara cholesterol 

3) Ana so kowane Dan Adam ya rika cin kwai saboda yana gina jiki 

4) Anaso a rika cin kwai saboda samarda lafiya a jikin Dan Adam 

5) Anaso a rika cin kwai saboda yana samar da kyan fata da saka jiki yin kyau sosai

6) Cin Kwai na bunkasa Kuzari da taimakawa dan adam aiwarta da aikin karfi ko motsa jiki 

7) Yana daga amfanin kwai shine yana kokarin dawowa da rasa ruwan jiki da kibar jiki kamar mutun yayi rashin lafiya kamar cholera  

8) kwai na taimakawa wajen lafiya kwakwalwa, da lafiyar idanu da gani sosai, sannan da gina jiki sosai. 

9) kwai yana Gina kashi da karama kashi karfi da lafiyar hakora  

10) Yana saka gashin jiki fitowa yanda yakamata da kara masa kyau, amfanin kwai ga mata Kenan musamman masu son karin gashi 


Wannan Sune amfani kwai ga lafiyar mace da namiji. Yana da muhimmanci koda sau daya ne a rana ku ci kwai 1, idan bakada halin cin kwai ko kudin siya to a rika cin awara ko kuma kwaida kwai wato (soya cake beans) don yana taka rawa sosai kusan kamar kwai. 


A darasin gaba za mu kawo muku amfani danyen ga mace, da kuma amfanin danyen kwai ga mace, sannan za mu kawo muku yadda ake yin hadin danyen kwai don amfanin mata da kuma illar shan danyen kwai ta hanyar da bata dace ba. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post