Alamomin So Ga Namiji Idan Yana Son Mace

Alamomin So Ga Namiji Idan Yana Son Mace
Alamomin So Ga Namiji


Alamomin so ga namiji, shine a koda yaushe yana baki lokacinsa a duk lokacin da kika bukaci hakan tabbas yana sonki ne.


Menene alamomin so ga namiji, idan yana son mace? Wannan itace tambayar da 'yan mata ke yi don su gane wane irin so samarin su ke yi musu, wane alamomin za su gane irin son gaskiya da suke yi musu. 


Akwai wasu mazan da basa iya tinkaran mace gaba da gaba su furta mata kalmar so. Ko kuma su fito fili su nunawa mace suna sonta. Sai dai su yi ta yin wasu halaye ko alamomin da mace idan mai hankali ce zata fahimci mai mata wadannan abubuwan sonta yake. Ga wasu manyan alamomin da mace zata iya fahimtar namiji yana sonta ba tare da ya furta mata ba.


Alamomin so ga namiji

1: Na Kusa dashi na sonki: Zaki ga abokansa da yan uwansa son jawo ki ajiki. Suna faran-faran dake. 


2: Zaki ga yana baki lokaci: Duk namijin da yake baki lokacinsa a duk lokacin da kika bukaci hakan tabbas yana sonki ne.


3: Son abunda kike so: yana daga cikin alamomin so ga namiji, Idan ra'ayinku yana zuwa daya yana son abunda kike so kuma yana kin abunda kike ki, akwai alamun yana sonki amma ya kasa furta miki.


4: Yawan yi miki kyauta: Zaki ga yana miki kyauta musamman da abunda yasan kin fi so ko sha'awa.


5: Yana yawan satar kallonki: Idan namiji yana ra'ayinki duk Inda kika shiga idanuwansa na kanki. Wannan yana nuna alamomin so ga namiji. 


6: Yana kokarin ganin ya burgeki: Idan namiji na sonki zai rika yin kokarin yi miki gwaninta ko da kuwa da kalmominsa ne.


Wannan sune kadan daga cikin alamomin so ga namiji, wanda idan yana son mace zata iya ganewa ta wannan hanyoyin. Ina fatan kun amfana daga wannan alamomin da kuka Karanta.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post