Alamomin namiji mai karfin sha'awa

Alamomin namiji mai karfin sha'awa
 Alamomin namiji mai karfin sha'awa


Wani bincike ya nuna cewa namji mai karamin kai yana da karfin sha'awa, irin su ake kira da harijai.


Menene alamomin namiji mai karfin sha'awa? Wannan itace tambayar da mata da yawa ke yi, musamman matan dake shirin yin aure, don suna son sanin namijin da za su aura yana da karfin sha'awa ne ko kuma baida ita. Hakan yasa a yau na kawo muku bayani da wasu alamomin namiji mai karfin sha'awa kamar yadda masana suka bayyana.


Kamar yadda ake iya ganin alamun mata masu karfin sha'awa suma maza akwai nasu alamomin. Sai dai abubuwan da za ku karanta ba lallai ne su iya zama tabbas ba, domin ana iya samun wasu mazan da wadannan alamomin da za mu bayyana muku wasu kuma ba lallai a same su dasu ba.


Alamomin namiji mai karfin sha'awa

Gane siffofin namiji mai karfin sha'awa abu ne mai sauki, kamar yadda masana suka bayyana. Ga alamomin kamar haka;


1) Namiji mai son zama cikin mata, yana daga cikin alamomin namji mai sha'awa idan yana yawan kasancewa cikin mata. Shi irin wannan namijin bai damu da zama cikin abokan sa ba, yafi son zama cikin mata don yin hira dasu ko jin dumin jikinsu yana sa yaji dadi.


2) Namji mai yawan kallon mace, idan kina da saurayi kuma kika ga duk sanda kuke tare yana kura miki ido yana kallon surar jikin ki yana nuna karfin sha'awa a tare dashi. Don idan ya samu dama zai iya kai hannu, sai ki kiyaye.


3) Wanda yake da jan idanu, masana sun ce idan kaga mace ko namji masu Jan ido yana nuna alamar hariji, sai dai masana lafiya sun Karyata hakan. Ana samun dan adam da jan ido wanda haka Allah ya halicce shi. wannan yana nufin ba lallai ne don an samu mace ko namji da jan ido ke nuna alamar karfin sha'awa ba.


4) Namji mai babban bura, akwai mazan da muddin suka Kalli mace koda ba irin wacce suke so ba za kaga gabansu ya mike, idan kuka Kalli wandonsa za ku ga burarsa ta Mike sosai.


5) Mai karamin kai, wani bincike ya nuna cewa namji mai karamin kai yana da karfin sha'awa, irin su ake kira da harijai. Don haka idan saurayinki na da karamin kai yana nuna shi hariji ne.


6) Mai karamin jiki, galibin namji mai karfin sha'awa an fi samun sirara marasa tsayi, a haka idan ka gansu za ka raina su ka yi tunanin babu abinda za su iya yi, amma kuma idan suka kasance da mace kai kace basu bane. 


Wannan sune wasu daga cikin alamomin namiji mai karfin sha'awa, sai dai duk wadannan abubuwan da muka bayyana suna iya zama gaskiya ko akasin hakan. Don babu wasu alamu na zahiri da gaskiya dake tabbatar da hakan. Allah ne ya barwa kansa sani.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post