Alamomin Matan Aure Masu Zina

Alamomin Matan Aure Masu Zina
alamomin mazinaciya

Masana sun bayyana alamomin Matan aure masu yin zina 


Zina babban laifi ne ga ma'aurata. Yana haifar da bacin rai, fushi da damuwa ga ma'aurata. A matsayin ka na miji idan kana zargin matarka na cin amanar ka, ga wasu alamomin da zaka gane matarka mazinaciya ce. 


Alamomin Matan Aure Mazinata 

- Nuna Rashin Gaskiya. Zata dinga boye wayar ta bata son ka dauka, sannan za ta dinga goge dukkan sakon dake kan wayar, ko ta canja passwords. Sannan zata dinga nesantar zama dakai tare da baka wasu uzurinta. 


- Canja Dabi'un ta. Shiga mai daukar hankali da yin kwalliya a lokacin da za ta tafi unguwa. Sannan kana iya ganin ta da sabbin kaya wanda ba kaine ka siya mata ba. Sannan za ka same ta da saka turaruka da sarkoki masu tsada da kuma yanayin sauyin irin abinda take ci da sha. Wanda ba kaine kake siya mata ba kuma ba sana'a take yi ba. 


- Za ta dinga nesantar yin Jima'i dakai. Yana daga cikin alamomin mazinaciya kauracewa mijinta yin jima’i. Ko kuma idan ta yarda ma babu wani nishadi da za ta ji, sannan za ta daina bayyana maka kalaman soyayya da ta saba yi maka a baya. 


- Neman Fada Da Rigima. Masana sun kara da cewa yana daga alamomin mazinaciya idan mace ta fiya yin fada da rigima a tsakaninta da mijinta har ta nuna baka yi mata komai. 


- Yawan Kashe Kudi. Idan ka samu matarka tana kashe kudi sosai kuma ba kaine kake bata ba sannan kuma ba wata sana'a take yi ba, sannan kana ganin ta da kyautuka wannan yana nuna mazinaciya ce. 


Wadannan sune wasu daga cikin alamomin matan aure masu zina(alamomin mazinaciya), amma basu ne tabbacin mace tana yin zina ba. Akwai dalilan da ke iya kawo abubuwan da muka bayyana kamar canjin rayuwa, damuwa, ko wasu abubuwan rayuwa. Mafi muhimmanci shine idan kana zargin matarka tana yin zina ka zauna da ita ka fuskanci matarka da halayenta  da gaskiyarta. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post