Alamomin Gane Akwai Aljanu A Tare Dake |
Yawan fushi da son kadaita, ki zauna ke kadai bakya san shiga mutane. Ki rinka jin haushin mutane haka kawai.
Akwai alamomi guda goma 10 da zaisa kigane akwai aljani a tare dake. Ga alamomin kamar haka;
1. Yawan faduwar gaba babu gaira babu dalili
2. Yawan fushi da son kadaita, ki zauna ke kadai bakya san shiga mutane. Ki rinka jin haushin mutane haka kawai.
3. Rashin san ibada ko kuma karatun al qur'ani kiji bakya san sauraro.
4. Yawan samun ciwon kai ko mara akai-akai.
5. Wani lokacin kiji ana raya miki sabon Allah a zuciyarki.
6. Mafarki barkatai. Mafarkin karnuka ko shanu ko mage ko kadangare, ko kuma ki rinka mafarkin kinyi aure ko kuma ga wani zai sadu dake, wani yazo a matsayin mijinki ko babanki ko kuma yayanki. Har ki rinka jin dadin saduwar a mafarkin. Wani lokaci ma kiyi mafarkin kina shayarwa ga jariri a hannunki.
7. Yawan mantuwa koda karatu ne, ko kuma wata magana, yanzu za'ayi dake yanzu zaki manta ta.
8. Yawan maganar zuci. Kiyi ta sake-sake kina warwarewa.
9. Ko kuma kiji kin tsani aure kiji bakyasan yin aure gaba daya, da an yi miki maganar sai ranki ya baci.
10. Yawan tsarguwa, koda wani abu akai bada keba kiji kin tsargu kamar dake akeyi,
Wadannan sune alamomin aljanu guda goma(10) dake nuna mace tanada jinnul ashiq ko kuma bakin jinnu.