Alamomin Da Ake Gane Akwai Jinnu A Jikin Mutum

Alamomin Da Ake Gane Akwai Jinnu A Jikin Mutum
 Alamomin Jinnu A Jikin Mutum 

Mutum yaji yafi son ya zauna shi kadai ba cikin mutane ba. Ya rinka jin haushin mutane.


Kadan daga cikin alamomin da ake gane akwai jinnu a jikin mutum. Akwai alamar fili da ta boye:-


Alamomi aljani a jikin mutum na fili

1. Mutum yaji baya son karatun al qur'ani

2. baya son sauraran sa, kuma baya san sallah.

3. Mutum yaji yafi son ya zauna shi kadai ba cikin mutane ba.

4. Ya rinka jin haushin mutane.

5. In yana labari ya saki labarin ya shiga cikin wani. Ko yawan son yin kuka, ko yawan dariya, ko zama a cikin datti, ko faduwar gaba da yawan Isoro.


Alamomi aljani a jikin mutum na boye 

Idan mutum yana barci ya rinka yin mafarke- mafarke, ko mutum yaji kamar ana binsa a baya in yana tafiya, ko kuma idan ya kwanta barci yaji kamar wani zaki a kusa dashi, ko kaji ana kiran sunanka batareda kaga kowa ba. Ko yawan mafarkai na halittu: mage ko bera ko jakuna. Ko mafarkin gaka a saman benaye ko chochi ko kuma makabarta. Ko mutum yayi mafarkin yana tashi sama, ko shanu sun biyo shi, ko cikin wuta. Ko kuma mace ta rinka mafarkin wani yana saduwa da ita wanda ba mijinta ba.


Wadannan sune kadan daga cikin alamomin da suke sanyawa agane mutum yana da jinnu a jikinsa.


Hanyoyin Fidda Jinnu A Jikin Mara Lafiya

Akanso kafin ka doshi mara lafiya to kayi alwala. Shima inda dama to ayi masa alwala. Sannan in cikin dakin akwai yara, to ayi kokarin basu kariya ta yadda idan jinnun sun fita ba zasu koma jikin su ba. Dan so tari in an fidda jinnu sukan fada jikin yaro in yana kusa, ko su zauna a cikin gidan. Don haka kafin a fidda su ya zama dole ayi kariya.


Yadda akeyin kariyar, ana kiran sallah sau uku a dakin sannan a karanta suratul zalzalati sau uku (3), sai abi kowace kasurwar dakin a karanta ayatul kursiyyu, tare da nuni gashi marar lafiya. Ya kuma kasance ko mace ce ko namiji akwai muharraminsa awajen, sannan sai kayi kokarin kare lafiyarka da ta iyalan mara lafiyar.


Addu'o'in Da Ya Kamata Ayi Kafin A Fara Yi Masa Magani Ko Karatu 


- أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ، بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مِعَ اسْمِهِ شَيْءٌ في الأرض ولا في السماء وهو السميع العليم.


أعوذ بكلمات اللَّهِ تَامَّاتِ مِن شَرِّ مَا لَق.


بسم الله على عقلي بسم الله على أفسي بسم الله على قلبي بسم الله على جميع بداى بسم الله على كُلِّ شَيْءٍ أَعْطا يه ربي.


- اللهم إني استوعك فسي وأهلي ومالي و ولدي. اللَّهُمَّ إِي أَسْتَوْ عَكَ لكي و واتم أعمالي.


- A'uzubillahi minash shaidanir rajim, bismillahil ladhi la yadurru ma'asmihi shai'un fil ardi wala fis samali wa huwas sami'ul aleem. (X3)


- A'uzhu bikalimatillahi tamatin min sharri ma khalaga (X3)


-Bismillahi ala aqali, bismillahi ala nafsi, bismillahi ala qalbi, bismillahi ala jami'i badani, bismillahi ala kulli shai'in a'danifi rabbi. (X3)


-Allahuruma inni astaudi'uka nafsi, wa ahli, ma mali, wa waladi. Allahumma inni astaudi'uka dini wa khawatimu a'amali.


Sannan sai a umurce mara lafiya da ya karanta suratul Ikhlas da Falaq da Nas. In kuma bazai iya ba sai ka dora hannunka akan mara lafiyar ka karanta masa. Sai kuma a karanta masa Ayatul kursiyyu da ayoyin karshe biyu na suratul Baqarah, sai suratul Ali Imrana ayats (17). suratul A'araf ayata (55), da ayoyi 1-10 cikin suratus Saffat, sai kuma suratul Jinnu daga farkon ta har karshenta.


Wadannan ayoyin dasu ake hada ruwan rukiyya a bawa mara lafiya ya rinka amfani dashi, don a raba shi da jinnun baki daya. Sannan kuma ana karantawa a tofa acikin man zaitun da man habbatus sauda, ya rinka shafawa yana sha cokali daya a rana.


Yadda Ake Hada Ruwan Rukiyya 

Ana samo ruwa tsaftatattu, ana so a samu ruwan zamzam, sai a samu bakar kanwa da farar albasa da kafur, a dauki yatsar mara lafiyar a saka aciki, sai a karanta wadannan addu'o'in a tofa aciki. Sannan a bawa mara lafiya ya shafe jikinsa, kuma ya cinye albasar. Sai a rinka yayyafa ruwan acikin dakin da mara lafiya ke kwana.


Mai Da AKe Son Mara Lafiya Yayi Amfani Dasu 

1. Man zaitun

2. Man ridi

3. Man habbatus sauda

4. Zaitu laus


Su za'a hade sai a karanta wadannan ayoyin da muka ambato, ya rinka shafawa a jikinsa in zai kwanta barci. Sau tari wasu jinnun basu zuwa jikin mutum sai zai yi bacci.


Abubuwan Da Ake So Mara Lafiya Yayi Amfani Dashi 

1. Garin habbatus sauda

2. Garin hantit

3. Garin khustil hindi

4. Garin za'afaran

5. Garin albabunaj

6. Garin daddawar batso


Su ake hadawa waje guda a saka musu miski, a rinka turaren jiki dashi da kuma dakin kwanan mara lafiya.


Addu'ar Neman Kariya Daga Sharrin Aljanu 

Yake 'yar uwa ko dan uwa, idan kinada matsalar da ta shafi jinnu, kafin ki dauki matakin fiddasu to ki dauki matakin kare kanki ta yadda in sun fita baza su dawo miki ba. Yayin da akayi wa me jinnu magana, to aljanun sukan taruwane su shawartawa junansu yadda kai kuma zasu cutar dakai. 


Ibn Abi Dunya ya fidda wani labari da ya samu wani bawan Allah acikin littafinsa ( AL-HAWATIF), daga Aisi Asmar. Yace wani mutum ya fito cikin dare yayin da zai gabatar da wata bukata tasa taurari sun haske duniya. Sai yaga wani gado da wasu al'umma sun kewaye gadon. Can sai yaga wani mutum yazo shi kadai sai mutanen suka tashi suka bashi gadon ya zauna shi daya. Sai yaji wannan nakan gadon yana cewa "yaya zamayı da urwatu ibn zubair? saboda ya matsa mana yana fiddamu daga jikin mutane" San sai yaji daya daga cikinsu yace; "kubarni dashi zanyi maganinsa".


Yace ina tsaye sai naga daya daga cikinsu ya bar cikin taron, yace ku jirani in dawo. Ko daya dawo sai yaji yace; "bazamu iya dashi ba yafi karfinmu. Saboda duk wayewar gari inya tashi sai ya fadi wata kalma, sai kuma da daddare nan ma yakan fadi wata kalma in zai kwanta".


Wannan mutum yace ina tsaye sai naji sunce; "yafi karfin mu" sai duk suka watse.


Wannan mutum yace sai na koma koda gari ya waye sai na saida kayana na sayi taguwa na tafi garin madina ina neman gidan Urwatu Ibn Zubair. Yace koda naje na sameshi na bashi labarin abinda nagani jiya da daddare, kuma na nemeshi daya gayamin kalmar dayake fada in ya tashi da safe da daddare da aljanu suka kasa shigarsa. Sai yace min ga addu'ar kamar haka:


" آمَنْتُ بِاللهِ وَحْدَهُ وَكَفَرْتُ بِالْجِبْتِ وَالطَّاغُوتِ وَاسْتَمْسَكْتَ بِالْعَرْوَةِ الْوَثْقَى لا فَصَامَ لَهَا وَاللَّهِ سَمِيعُ العَلِيمُ"


"Amantu billahi wahdahu wa kafartu bil jibti waddaguti, was tumsiktu bil urwatul wuthqa lanfisama laha, wallahu sami'ul aleem".


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post