Alamomin cikakkiyar budurwa wadda bata taba sanin namiji ba

Alamomin cikakkiyar budurwa wadda bata taba sanin namiji ba
Alamomin cikakkiyar budurwa 


Hanyoyin gane mace cikakkiyar budurwa wadda bata taba sanin da namiji ba 


Gare ku 'yan mata da matan aure da samari yakamata kusan wannan domin zai amfane ku. Wannan sakon ya kunshi:


  1. Dalilin da ke jawowa 'yan mata yawan ciwon ciki ko mara musamman bayan Haila
  2. Yanda ma'aurata zasu yi 'family planning' ba tareda shan magani ba.
  3. Abinda ke fitowa wasu mata mai kamar majina, da sauransu. Abu Albani;


Da farko, zan yi amfani da kalmomin hausa domin samun sauqin fahimta, kalmomin turancin da ban san ma'anar su da hausa ba zan yi kwatancen da za'a gane.


Idan nazo kan 'family planning zan yi bayani akan abinda bincike ya tabbatar, amma ba sai na maimaita ba, Allah Ya kan iya canja ikonsa koda anyi hakan kuma a samu haihuwa, amma Insha Allah ba'a cika samun haihuwa ba idan akayi hakan.


A jikin mahaifar mace, (female reproductive system) idan kuka lura, zaku ga wasu abubuwa kamar hannu guda biyu, daya gefen dama dayan kuma gefen hagun, a bakin ko wanne akwai wani abu qullutu wanda a cikin sa akwai wasu kwayaye.


Duk sanda Mace tayi Jinin ta na Haila, bayan Jinin ya dauke da kwanaki 14, wancan abu da muka ambata yana sake wadancan kwayaye, wadanda sune sinadarin da ake hadawa a samu da.


Wadannan kwayaye idan aka sake su sukan shiga cikin mahaifar mace su yi kwanaki 2 (48 hours) daga nan idan babu abinda yazo ya taba su (maniyin Namiji) to zasu mutu.


Kafin a sake wadannan kwayaye akwai abinda Allah Ya halitta a cikin mahaifar mace wanda zai zo ya share mahaifar ta sosai, domin mahaifar zatayi bako, wanda shine kwayaye kenan.


Akwai wasu jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da hagu na mahaifar mace, idan akazo aka share mahaifar, to wadannan jijiyoyin zasu cika da jini sosai, sai su koma ja-ja-wur, suna jiran wannan bakon da zai shigo mahaifa idan ya girma bai mutu ba sai suke bashi jinin nan a matsayin abinci.


Maniyyin da Namiji yana yin kwanaki 3 (72 hours) a cikin mahaifar mace kafın ya mutu.


Idan mun fahimci wadancan bayanan, to yanzu sai mu hada su waje daya muga yadda abin yake. Idan Mace ta gama haila da kwanaki 14 to wancan abin kamar tiyo na jikin mahaifar ta yakan sake wadannan kwayaye, zasu shigo cikin mahaifar ta suna jiran Maniyyin Namiji yazo ya same su, idan suka hadu, kuma komin karancin Maniyyin nan, to Maniyyin zai zamo musu kamar taki don haka zasu hadu su girma, da hakane kuma Allah zai yita sallafa shi har ya maida shi mutum.


To idan babu wani Maniyyi da ya shigo gurin a dalilin rashin saduwa da mace, to wadannan kwayaye zasu mutu bayan sunyi awa 48 (kwanaki 2), idan kuma suka mutu to zasu biyo cikin al'aurar mace sai su fito, sai kaji Mata na tambayar sukan ga wani abu mai kamar majina-majina yana fito musu a al'aura, wannan shine abinda ke fitowar, wannan ya sa Malamai suka ce babu komai akan wannan kawai ta wanke shi ba shida wani hukunci.


A dalilin rashin shigar Maniyyi da zai girmar da wancan kwai, sai wadancan jijiyoyi da suka tara jini a cikin su, sai suyi wani abu da ake kira fushi, basu ji dadi ba, a dalilin haka sai suke kartar jikin mahaifar mace, sai kaji mace tace maka tana yawan fama da ciwon mara musamman idan ta gama Haila.


Anan zamu fahimci rashin aure (alamomin cikakkiyar budurwa) ke jawo wannan, kuma maganin haka shine aure ko tiyata.


Idan karce jijiyoyin nan yayi yawa kuma aka yi rashin sa'a sai su fashe, idan kuma suka fashe sai jini yayita fita ba tsayawa, wannan shine ake kira da jinin Istihada, daman Manzon Allah (s.a.w) ya gayawa wata mata cewar ai wannan jinin jijiya ne.


Idan Matar aure ce kuma tana son yin 'family planning' da Mijinta, to hanya mafı sauki itace; kamar yadda muka ji bayan gama hailar ta da kwanaki 14 ake sake wadancan kwayaye, kuma sukan yi kwanaki 2 kafım su mutu, shi kuma Maniyyi yakan yi kwanaki 3 kafın ya mutu, to su ma'auratan kada su sadu tun ranar 12 da gama hailar ta, har sai bayan ranar 16 da gama hailar ta.


Ki dan tsaya kadan anan kafın ki cigaba kiyi tunanin meyasa akace haka?


Dalilin hakan kuwa shine, ranar 14 kwai ke zuwa, to idan suka sadu ranar 12, kada mu manta Maniyyi sai yayi kwanaki 3 kafın ya mutu, to kunga idan suka sadu ranar 12, maniyyin nan yananan a mahaifar yana jiran a sake kwai, zai zauna na tsawon kwanaki 12,13,14 kafın ya mutu, to kunga zasu ci karo ranar 14, kuma babu abinda zai hanashi sarrafa kwayaye nan. Ance har sai bayan ranar 16 ne saboda shi kuma kwai yakan yi kwanaki 2 kafın ya mutu.


To wadannan kwanaki 5 din-12,13,14,15,16 da gama Hailar mace, su ake kira da 'danger periods' ma'ana kwanaki masu hatsari, an kira su da hakane saboda idan dai aka sadu da Mace a wadannan kwanakin to kuwa tabbas zata samu ciki, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki, kuma idan ma'aurata na son yin 'family planning' wadannan kwanakin zasu kauce wa saduwa, ba sai sun sha magani ba, sai dai idan Mulkin Ubangiji ya shigo ciki.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post