Alamomi 5 Idan Mace Na So A Yi Jima'i Da Ita

Alamomi 5 Idan Mace Na So A Yi Jima'i Da Ita
Alamomi son Jima'i ga mace 
 

Wasu lokutan ma idan mace na son mijinta ya sadu da ita ba ta sanin tana bayyana wadannan alamomin


Idan mace na son a yi jima’i da ita tana iya bayyanawa ta hanyar kalamai. Amma wasu matan kuma Kunya na iya hanasu bayyanawa mazajensu suna da bukatar su, tana iya nuna maka alamomin ta hanyar jikin ta. 


A Wannan rubutun zan bayyana muku wasu alamomi da mace ke nunawa idan tana son namji ya kusance ta. Fahimtar hakan ga namji yana da muhimmanci domin zai taimaka masa fahimtar yanayi da lokacin da matarsa ke bukatar jima’i. 


Wasu lokutan ma idan mace na son mijinta ya sadu da ita ba ta sanin tana bayyana wadannan alamomin, amma kai idan ka fuskanci hakan sai kai kokarin yin abinda ya dace don ganin ka biya mata bukatar ta. 


Alamomi 5 Idan Mace Na So A Yi Jima'i Da Ita

Ba tare da na cika ku da surutu ba, bari mu tafi kai tsaye na bayyana muku wasu daga cikin alamomin da mace ke nunawa idan tana bukatar jima’i daga wajen mijinta. 


1) kusantar Jikin Namji; Idan kaga mace na son kasancewa a kusa dakai, ma'ana zama kusa da inda kake wanda ba ta saba yin hakan ba. Kuma idan kaga tana jingina da jikin ka tana sakin jikinta a jikin ka, alamu ne dake nuna so take ka yi jimai da ita, amma Kunya ya hana ta bayyana maka kai tsaye. Idan kaga irin hakan sai ka yi kokarin yin abinda ya dace. 


2) Tsokana; Idan kaga matarka ta takura maka da wasannin tsokana, irin wasan miji da mata ko kuma yi maka wasu abubuwan da ta san yana saka nishadi da zai jawo hankalinka kaji ka kusance ta. Da yi maka yawan murmushi duk alamun so take ka kusance ta. 


3) Yawan Nishadi Da Farin Ciki; Idan Kaga mace tana cikin farin ciki ba tare da ka yi mata wata kyauta ba, yana nuna so take ka kusance ta. Za ka ji tana yi maka zantuka masu ban dariya, da zarar kaga haka yi kokarin ka fara yi mata wasanni motsa mata sha'awa kafin fara Jima'i. 


4) Kebewa; Idan kun saba zama da mace a falo musamman idan ba cikin dare bane, kaga tana kwance a kan gado ba tare da wata rashin lafiya ba, wannan yana nuna alamun bukatar ta Jika a kusa da ita don yin jima’i. 


5) Kwalliya; Idan kaga mace ta caba ado ta yi kwalliya ta yi shiga mai kyau kuma ba unguwa za ta je ba, Sannan kuma ta fesa turare mai daukar hankali, kai kasan ba sai an sanar dakai tana cikin bukatar son yin Jima'i ba. 


Wadannan sune wasu daga cikin bincike da aka gudanar kan alamomin da mace ke nunawa a lokacin da take son mijinta yai Jima'i da ita amma ba za ta iya bayyana masa ba. Sai dai ba duka matan aure ke yin hakan ba, wasu ai babu Kunya tunda tsakanin miji da mata an zama daya tana iya bayyana masa duk lokacin da take bukatar sa. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post