Addu'ar Tsari Daga Kambun Baka Ko Maita Ko Sihiri Ko Miyagun Aljanu

Addu'ar Tsari Daga Kambun Baka Ko Maita Ko Sihiri Ko Miyagun Aljanu
Addu'ar Tsari Daga Kambun Baka Ko Maita Ko Sihiri Ko Miyagun Aljanu 


Akanso duk macen da ta haihu ko ya yaronki yake ko 'yar ki take kafin a fara zuwa barka to kimata wannan hadin


Dayawa daga cikin yaranmu kambun baka yana damunsu batare da mun sani ba, wasu kuma sihiri ne, wasu kuma tun daga haihuwarsu suke gamuwa da kambun baka ko maita. Da zarar an haifi yarinya ko yaro mai fasali sai mutane suyi ta magana wasu ma ba tare da sun hada da tabarakallah masha Allah ba. Irin hakane sai aga yaro ya lalace saboda wata kallonsa kawai zatayi tace 'dubi yaro mai kyau' ko kuma 'dubi yarinya kyakkyawa'.


Daganan sai aga yarinya ta lalace har karshen rayuwarta idan ba sa'a akayi ba. Akanso duk macen da ta haihu ko ya yaronki yake ko 'yar ki take kafin a fara zuwa barka to kimata wannan hadin:


Man alayyadi

Man ridi

Man hulba

Man kwakwa


Sai ki hadesu ki kuma karanta wannan addu'ar a cikin man a rinka shafawa yaron ko yarinyar idan anyi wanka. Ga addu'ar kamar haka;


- سورة الفاتحة


- سورة البقرة آية 5-1


- سورة البقرة آية 255


- آخر سورة البقرة


- سورة الكهف آية 10-1


سُورَةُ الصَّافات آية 10-1


سُورَةُ الْفُرْقَان آية 23-22


سورة الأنبياء آية 18-17


- سورة يونس آية 83-81

  - Suratul Fatiha

  - Suratul Baqarah ayata 1-5

- Suratul Baqarah ayata 255

- Karshen suratul Baqarah

 - Suratul Kahfi ayata 1-10

- Suratus Saffat ayata 1-10

-Suratul furqan ayata 22-23

- Suratul Anbiya'i ayata 17-18

-Süratu Yunus ayata 81-83


Sai kuma ki karanta wannan addu'ar kamar haka;


" اللَّهُمَّ إِنِّي أستودعك نفسي وأهلي وذريتي و ديني و طريقي و عرضي


وَ مَالِي وَ كُلَّ من انتمني إلى و من أحبه و ماله يا حفيظ يا واقي يا كافي -


فسيكفيكهم الله وهو السميع العليم"


"Allahumma inni astaudi'uka nafsi wa ahli wa zhurriyati wa dini wa dariqi wa ardi wa mali, wa kulli man tamanni ilayya, waman uhibbuhu wa malahu ya hafizu ya waqi ya kafi-fasayakfikahumul lahu wa huwas sami'ul aleem".


Wannan itace addu'ar da za'a tofa acikin mayukan, yazamana ana shafawa jaririn idan anyi wanka. Babba ma zai iya shafawa. Wannan hadin zai gyara wa mutum fata tayi laushi sannan zai masa magani daga kambun baka ko aljanu ko sihiri da yardar Allah S.W.T.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post