Addu'ar Neman Rufin Asiri Da Wadatar Zuciya |
Akanso a samu mace da wadatar zuciya da kauda kai daga abinda ba naki ba. Koda anyi maki gori da abinda bakida shi, zinari ko azurfa ko kuma sufofi. Sai kiyi koyi da addu'ar da Manzon Allah SAW ya koyar ga daya daga cikin sahabbansa mai suna Shaddadu Ibn Aws. yace: "Ya Shaddadu in kaga mutane suna rige-rige na tara zinare da azurfa, kai kada ya dameka. Kayi kokarin rike wadannan kalmomi, zasu gama wahalarsu su dawo su same ka cikin rufin asiri" Ga kalmomin kamar haka;
" اللهم إني أسألك الثبات في الأمر والعزيمة على الرشد وأسألك شكر نِعْمَتِكَ وَحُسْن عبادك. وأسألك قلبا سليما ولسانا صادقا وأسألك من خير مَا تَعْلَمُ واعوذ بك من شر ما تعلم واسْتَغْفِرُكَ لِمَا تَعْلَمُ إِنَّكَ أَنتَ عَلامُ
الغيوب".
Allahumma inni as'alukath thabatu fil amri, wal azimatu alar rushdi, wa as'aluka shukra ni'imatika wa husna ibadika. Wa as'aluka qalban saliman wa lisanan sadiqan. wa asaluka min khairi ma ta'alam wa a'uzubika min sharri ma ta'alam wa astagfiruka lima ta'alam. Innaka anta allamul gayub".
Da zakiyi ko zakayi kokarin karanta wannan addu ar to har abada asirinki bazai tonu ba.