Addu'ar Neman Biyan Bukata

Addu'ar Neman Biyan Bukata
 Addu'ar Neman Biyan Bukata 

Duk yadda makiyi zai taso ki gaba ko makiya, don sau tari mata suna samun kansu a irin wannan yanayin har ya kaisu ga zuwa wajen bokaye ko kuma zasu shiga gidan miji mai mata. 


Yake 'yar uwa da wani abu zai sameki na bacin rai. ko ki rasa gane inda mijinki yasa gaba, maimakon ki dauki kudinki ki kaiwa malamin tsubbu ko boka ya raba ki da imaninki da kuma dukiyar ki da mutuncin ki, ki dauki wannan addu'a da Manzon Allah SAW ya kira ISMULLAHIL A'AM. acikin sahihul Muslim, hadisin Anas Ibn Malik:


" اللهم إني أسألك بأن لك الحمدُ لاإله إلا أنت يا بديع السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يَا

ذا الجلال والإكرام يا حي يا قيوم"


"Allahumma inni as'aluka bi anna lakal hamdu la'ilaha illa anta. ya badi'us samawati wal ardi, ya zal jalalu wal ikram, ya hayyu ya qayyum".


Ki yawaita karanta wannan addu'ar, zata zame miki babban jigo a rayuwarki.


Addu'ar Samun Rinjaye Ga Makiya 

Duk yadda makiyi zai taso ki gaba ko makiya, don sau tari mata suna samun kansu a irin wannan yanayin har ya kaisu ga zuwa wajen bokaye ko kuma zasu shiga gidan miji mai mata. Duk matar da take son tayi galaba akan makiyanta to ga addu'ar da zata lazimci karantawa. An samo daga cikin Sunanu Abu Dawuda da Nasa'i da Abu Musa daga Manzon Allah SAW. yace: Manzon Allah SAW in zai tunkari makiyansa yana karanta wannan addu'ar. Don haka kuma ku rinka karanta ta:


" اللهم إنا نجعلك في نحورهم ونعوذبك من شرورهم".


"Allahumma inna naj'aluka fi nuhurihim wa na'uzhu bika min shururihim"


Ko gidan aure za'a kaiki kishiya tayi miki barazana sanda zaki shiga gidan, idan kika karanta wannan addu'ar in Allah ya yadda baza tayi nasara akan ki ba.


Addu'ar Samun Rinjaye Ga Makiya kashi Na biyu 2

Itama wannan addu'ar in har zaki lazimci yinta to makiya ko makiyi baza su taba yin rinjaye akanki ba. Ibn Hajar ya ambace ta cikin littafinsa


(Majmuzzaweed). Ga addu'ar kamar haka:


" يا مالك يوم الدين إياك نعبد وإياك نستعين".


"Ya maliku yaumuddin iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in".


Wannan addu'ar tanada matukar amfani wajen ruguza makiya.


Addu'ar Samun Rinjaye Ga Makiya kashi na uku 3


" اللهم أنت عبدي وانت ناصر وبك أقاتل".


"Allahumma anta abadiy wa anta nasiri wabika uqatil".


Addu'ar Samun Rinjaye Ga Makiya na hudu 4


Ki karanta ayata 249 acikin suratul Baqarah.


ربنا افرغ علينا صبرا وثبت أقدامنا وانصرنا على القوم الكافرين".


"Rabbana afrig alaina sabran wa thabbit aqdamina wansurna alal qaumil kafirin".


Addu'ar Samun Rinjaye Ga Makiya kashi Na Biyar 5


"لا إله إلا الله الحليم الكريم سُبحانَ الله رَبُّ السَّماوات السبع ورَبُّ العَرْش


العظيم لا إله إلا أنت عز جارك وجل ثناؤك ولا إله غيرك".


"La'ilaha illallahul halimul karim, subhanallahi rabbis samawatis sab'i wa rabbul arshil azim, la'ilaha illa anta azza jaruka wa jalla thana'uka wa la'ilaha gairuka".


Addu'ar Samun Rinjaye Ga Makiya kashi na Shida 6


Cikin Sahihul Bukhari da Ibn Abbas:


حسبنا الله ونعم الوكيل ".


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil


Itace addu'ar da Annabi Ibrahim AS yafada a lokacin da aka jeta shi cikin wuta. Allah SWT ya umurci wutar da tayi sanyi.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post