Addu'ar Maganin Baki Ko Kambun Baka |
Anaso daga uwa idan ta haihu duk lokacin da zata bada yaron ga wani ta rinka karanta masa wannan addu'ar;
" أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِن كُلِّ شَيْطَا وَهَمَاتٍ وَمِن كُلِّ عَيْنٍ لَامَةٍ"
"A'uzu bi kalimatillahi tamatin min kulli shaidanin wa hammatin wamin kulli ainin lama".
Addu'ar Neman Shiriya Ga Yara
Anaso ga uwa in ta haifi yaro ta rinka karanta masa wannan addu'ar. Yake uwargida in har kina karantawa yaranki wannan addu'ar, to Insha Allahu zai kare su daga afkawa tarkon zamani, bazasu zama mazinata ba. ko mashaya, ko barayi, da dai sauran mugayen halaye ba Insha Allahu.
Ki rinka karanta kafa bakwai ki tofa a hannunki ki shafa ajikin yaron ko yarinyar da kika haifa. Ga addu'ar kamar haka:
" أعُوذُ بِكَلِمَاتِ الله التامة من شر ما لق. أعوذ بكلمات الله التامة من غضبه وعقابه وشر عباه ومن همزات الشياطين وا يحضرو "
"A'uzu bikalimatillahi tamati min sharri ma khalaqa. auzu bikalimatillahi tamati min gadbihi, wa iqabihi, wa sharri ibadihi, wa min hamazatus shayadin wa an yahdurun".
Addu'ar Neman Haihuwa
Yake 'yar uwa kada ki yanke tsammani in kinga lokaci yayi tsawo baki samu haihuwa ba, to kada ki yanke tsammani daga rahamar Allah. Kada kuma ki saida mutuncin ki wajen bin 'yan bori da 'yan tsubbu, kiyi imani da Allah kuma ki dogara dashi. Ki lazimci yin addu'ar da Annabi Zakariya'u AS yayi. Ki tashi tsakar dare kiyi nafila raka'ah biyu ki rinka karanta wannan addu'ar:
رب هب لي من لدنك ذرية طيبة إنك سميع الدعَاءِ رَبِّ لَا تَدْرْنِي فَرْدًا
و أنت خير الوارثين"
"Rabbi habli min ladunka zurriyatan dayyiba innaka sami'ud du'a rabbi la tazarni fardan wa anta kharrul warithin".