Addu'ar Karya Sihiri kowane iri |
Daga cikin nau'o'in sihirin akanyi sihiri domin miji ya tsani matarsa, ko ke mace kiji kin tsani mijin, ko miji yaji baya sha'awar matarsa ko in ya shigo dakinki da niyyar ya sadu dake yaji wani wari kamar jaba, ko kuma ayi sihiri a saukarwa mace jini ba tsayawa, ko asa mahaifi ya tsani 'ya'yanki, ko ayi asirin da za'a kangarar da yaranki su ringa sata da shaye-shaye da-sauran kangara
Yake 'yar uwa müsulma, idan kina zargia anyi miki sihiri, an shiga tsakaninki da maigidanki, ko kina ganin kamar anyi sihiri ne domin a raba tsakanin 'ya'yanki da mahaifinsu. To ga hanyar da zaki bi ki warware shi ba tareda kinje gurin boka ko malamin tsubbu ba Insha Allah.
Daga cikin nau'o'in sihirin akanyi sihiri domin miji ya tsani matarsa, ko ke mace kiji kin tsani mijin, ko miji yaji baya sha'awar matarsa ko in ya shigo dakinki da niyyar ya sadu dake yaji wani wari kamar jaba, ko kuma ayi sihiri a saukarwa mace jini ba tsayawa, ko asa mahaifi ya tsani 'ya'yanki, ko ayi asirin da za'a kangarar da yaranki su ringa sata da shaye-shaye da-sauran kangara. Ko a hana budurwa aure da dai sauran nau'i na sihirce-sihirce. Ko asirin da ake kira 'dan baka', in mijinki ya shigo dakinki yaji ya zama kamar mace 'yar uwarki baya iya yin komai.
Da farko zaki samu ganyen magarya guda bakwai (7) sannan ki samo duwatsu masu dan girma guda biyu (2) sai ki nika ganyen magaryar akan duwatsum. Ko kuma ki daka a turmi duk dayane
Ki samo ruwa a kwano ki juye ganyen magaryar kiyi kyakkyawar alwala ki zauna ki natsu, kiyi bismillah da ta'awwizi ki karanta Suratul Fatiha kafa bakwai (7) kowacce in kin kai karshe ki tofa acikin ruwan. Sannan ki karanta wadannan ayoyin kamar haka:
- سورة البقرة آية 255
سورة الأعراف آية 122-117
سورة يونس آية 82-79
سورة الضحى آية 70-65
- سورة الكافرون
- سورة الاخلاص
- سورة الفلق
- سورة الناس
Suratul Baqarah ayata 255 (x7)
Suratul A'araf ayata 117-122 (x7)
Suratu Yunus ajata 79-82 (x7)
- Suratud Duha ayata 65-70 (x7)
Suratul Kafirun (x7)
Suratul Ikhlas (x7)
Suratel Falaq (x7)
Suratan Nas (x7).
Zaki karanta ki tofa duk acikin ruwan nan dakika zuba ganyen magarya. In kin gama sai ki debi ruwan da tafukan hannayenki guda biyu ki sha sau uku, ki kuma shafe ko ina a jikinki da ruwan sosai. Sannan wadannan ayoyin ki tofa su acikin man ridi da man habbatus sauda ki rinka shafawa.
Kullum zakiyi haka kamar yadda kikayi na farkon har kwana bakwai (7). To Insha Allahu duk sihirin da aka yi maki zai lalace. Sai ki kula da cin dabino ajwad guda 7 a kowace rana da asuba. Da yardar Allah duk wani sihiri da za'a maki ba zai yi tasiri ba, in kuma anyi zai lalace Insha Allahu.