Addu'ar Da Muslimi Zai Yi A Lokacin Yaga Abin Tsoro Ko Abinda Yasa Shi Bakin Ciki

Addu'ar Da Muslimi Zai Yi A Lokacin Yaga Abin Tsoro Ko Abinda Yasa Shi Bakin Ciki
Addu'ar yaye bakin ciki


Addu'ar Da Yakamata Mutum Ya Yi Lokacin Da Yaga Abin Tsoro Ko Abinda Yasa Shi Bakin Ciki 


Annabi (SAW) yace, wanda ya karanta Ayatul kursiyyu da ayoyin karshe na suratul baqara yayin da wani bakin ciki ya same shi, to Allah (SWT) zai kawo masa sauki.


Annabi (SAW) ya kasance idan wani abu yabata masa rai yakan ce;

"لا إِلَهَ إِلَّا اللهُ الْحَلِيمُ الْكَرِيمُ سُبْحَانَ اللهِ رَبِّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ"

"La ilaha illallahu alhalimu alkarimu, subhanallahi rabbil arshil azim, alhamdulillahi rabbil alamin".


1. Addu'ar Yaye Fushi 

"لا إله إلا اللهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ رَبَّ السَّمَاوَاتِ وَ رَبُّ الْأَرْضِ وَ رَبُّ الْعَرْشِ الْكَرِيمِ"


"La ilaha illallahul azimul halim, la ilaha illallahu rabbul arshil azim, la ilaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kareem".


2. Kalmomin Farin Ciki 

Mutumin da ya samu kansa cikin damuwa Ko wani Tashin hankali, ya rasa abinda yake damunsa a duniya sai ya karanta wannan addu'ar;


" لا إِلَهَ إِلَّا اللهُ الْحَلِيمُ الْكَرِيمُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ رَبَّ

السَّمَاوَاتِ السَّبَعِ وَ رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ"


"La ilaha illallahul halimul karim, la ilaha illallahul aliyyul azim, la ilaha illallahu rabbus samawati wa rabbul arshil azim".


Insha Allah duk wata damuwa da yake ciki zata zama tamkar tarihi.


3. Addu'a Ta Musamman

Anaso a rinka karanta wannan addu'ar koda sau daya ne a rana, tanada mahimmanci sosai. Abu Hanifa RA yace, yayi mafarki da Allah SWT sau 99, sai yace in yasake yin mafarki da Allah zai tambayeshi wacce addu'a ce bayinsa za su rinka karantawa ya tsaresu daga azabar lahira. Randa yayi mafarkin na cikon 100 sai ya tambayi Allah SWT ya sanar dashi addu'ar da idan bawa yana karantawa Allah zai tsareshi daga azaba, koda yana aikata wani sabo Allah SWT zai masa arzikin tuba kafin ya mutu. Don haka a mafarkin sai Allah SWT ya gaya masa addu'ar kamar haka;


سُبْحَانَ اللَّهِ وَاحِدُ الْأَحْدُ, سُبْحَانَ اللهِ فَرْدُ الصَّمَدُ سُبْحَانَ اللَّهِ رَفَعَ السَّمَاوَاتِ بِغَيرِ أَمَدٍ سُبْحَانَ اللهِ مَن لَّمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ

"Subhanallahi wahidil ahad, subhanallahi fardus samad, subhanallahi rafa'as samawati bi gairi amadin subhanallahi man lam yalid walam yulad" walam yakun lahu kufwan Ahad". Anaso in zaka kwanta ka karanta koda sau daya ne.


4. Addu'a Ta Musamman II

Wannan addu'ar duk wani halin damuwa daka samu kanka, ko wane kuncin rayuwa, ko neman aiki ko neman mijin aure. Kai koma mai kakeso karkayi kasa a gwiwa. Muddin zakiyi/zakayi wannan addu'ar Allah SWT zai kawo maka sauki acikin al'amuran ka. Ana so kiyi wannan addu'ar da iklasin Allah. Ga addu'ar kamar haka;


- حَسْبُنَا اللَّهُ سَيُؤْتِينَا اللهُ وَرَسُولُهُ مِنْ فَضْلِهَ إِنَّا إِلَى اللَّهِ رَاغِبُونَ


رَبَّ إِنِّي لِمَا أَنْزَلْتَ إِلَيَّ مِنَ خَيرٍ فَقِيرٌ


- رَبِّ إِنِّي مَغْلُوبٌ فَانْتَصِرْ


- رَبَّ لَا تَذَرْنِي فَرْدًا وَ أَنْتَ خَيْرُ الْوَارِثِينَ


- لا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ الْعَلِيَّ الْعَظِيمِ


- لا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ


- Hasbunallahu sayu'tinallahu wa rasuluhu min fadlihi inna ilallahi ragibun

Rabbi inni lima anzaltu ilayya min khairin faqir

- Rabbi anni maglubun fantasir

Rabbi la tazirni fardan wa anta khairul warithin

- La haula wala quwwata illa billahil aliyul azeem

- La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minzal zalimin.


Wannan addu'ar kamar a magani ne ace anti biotic, duk irin matsalar da kake ciki zaka iya karanta ta. Akanso wannan addu'ar in ka shiga cikin damuwa kana neman wani abu a wajen Allah SWT, karasa yadda zakayi. Anaso katashi cikin dare kayi nafila raka'ah biyu ko hudu koma duk yadda tasamu sai ka karanta addu'ar.


5. Addu'ar Neman Biyan Bukata 

Wannan addu'ar akanso ayita bayan kayi raka'ah biyu kafin sallar asuba. Ibn Abbas RA yace, 'Babana ya aikeni wajen Manzon Allah SAW, sai naje na same shi a dakin 'yar uwata Maimuna. Ko da taje na samu yayi raka'atanul fajr sai na jirashi. Kafin yamin magana sai naji yayi wannan addu'ar kamar haka:


" اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ رَحْمَة من عندك تهدي بها قلبي, وَ تَجْمَعُ بِهَا شَمْلِي. وَتَلُومُ بِهَا شِعْتَى وَتَرُدُّ بها الفتن على. وتصلح بها ديني. وتحفظ بها غَائِبِي وَتَرْفَعُ بِهَا شاهدي وتزكى بها عملي. وتبيض بها وجهي. وَتَنْهُمُنِي بِهَا رُشْدِي. وَتَعْصِمُني بها من كل سوء. اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ


والعافية في الدنيا والآخرة"


"Allahumma inni as'aluka rahmatan min indika tahdi biha qalbi, wa tajma'u biha shamli, wa talumu biha sha'athi, wa turaddu bihal fatni anni, wa tuslihu biha dini, wa tahfazu biha ga'ibi, wa tarfa'a biha shahidi, wa tuzakki biha amali.wa tabyad biha wajhi, wa tulhimni biha rushdi, wa ta'simuni biha min kulli su'in, allahumma inni as'alukal afwa wal afiyata fid dunya wal akhira".


Anaso duk abinda kake nema wajen Allah kasa shi aciki. Kasuwancinka ne ya lalace, aiki kake nema, mijin aure kikeso, koma dai menene sai ka gaya wa Allah damuwarka da yaqinin Allah zai amsa maka.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post